- Lauyan dake kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya cewa Kamfanin NNPCL ba shi da hurumin tsayarwa ko daidaita farashin man fetur.
- Falana ya cewa ikon kayyade farashin man fetur yana hannun shugaban kasa Bola Tinubu.
- A ranar 31 ga watan Mayu, kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa ya daidaita farashin man fetur a kasuwannin sa.
Lauyan dake kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya yi ikirarin cewa Kamfanin Mai na Najeriya NNPCL ba shi da hurumin tsayarwa ko daidaita farashin man fetur,kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Falana ya dage cewa ikon kayyade farashin man fetur yana hannun shugaban kasa Bola Tinubu, domin babu wani kwakkwaran ministan albarkatun man fetur.
KARANTA WANNAN: Tallafin Fetur: Za Mu Sake Duba Mafi Ƙarancin Albashi Don Yin Tunani Na Gaskiya — Tinubu
A ranar 31 ga watan Mayu, kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa ya daidaita farashin man fetur a kasuwannin sa.
Kakakin kamfanin na NNPC, Garba Deen Muhammad, ya bayyana dalilin da ya sa aka daidaita farashin.
Amma da yake magana a wata hira da gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, Falana ya ce ya saba wa doka yadda kamfanin NNPC ko kuma wadanda ake kira “Rundunar Kasuwar da ba a iya gani” ke kayyade farashin man fetur.
“Hukumar NNPC ta koma wani kamfani mai iyaka. Yanzu haka shine NNPC Limited. Har ila yau, kamfanonin NNPC kamar Total, Exxonmobil, da Shell da ke aikin harkar mai ba za su iya bayyana karin farashin man fetur ba.
“Wannan aikin ya rataya a wuyan gwamnati ne.
“Babu wanda ke da hakkin a Najeriya ya sanya farashin man fetur in ba gwamnati ba, kana da dokar kayyade farashin man fetur, yanzu PIA,” in ji Falana.
A wani labarin kuma, Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa
Wata babbar kotu dake Makurdi ta tabbatar da korar Iyorchia Ayu daga matsayin shugaban PDP na kasa.
A cewar mai shari’a Ikpambese, Ayu ba zai iya cigaba da zama a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa ba.
Daukar matakin ya biyo bayan dakarwar da kwamitin zartarwar PDP reshen jihar Benuwe ya yiwa Ayu bisa rashin biyan hakkokin mambobinsa