Gwamnatin jihar Yobe ta gudanar da Taron tallafin karatu ga ‘yan jihar Yobe da yake magana bayan halartar Taron Sanata Uba sani Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijan Nageriya Ya tabbatar da kudrin na Gwamnatin jihar Yobe inda ya bayyana cewa A safiyar yau ne na bi sahun Shugaban Majalisar Dattawa, Mai Girma Dokta Ahmad Lawan da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da Kyaftin din Masana’antun Kwararru kan Ilimi, da Wakilan Hukumomin ci gaba da sauran jiga-jigan ‘yan Nijeriya a wajen taron bayar da tallafin karatu na Jihar Yobe. wanda ya gudana a dakin taro na Ladi Kwali, Sheraton Hotel dake Abuja.
Gwamnatin jihar Yobe ta hada taron ne domin samar da kudaden da za su taimaka wajen farfado da harkar ilimi a jihar Yobe wanda ya fuskanci koma baya sakamakon tabarbarewar ayyukan tada kayar baya.
Jihar Yobe na daga cikin jihohin arewa maso gabas da suka sha fama da hare-haren ta’addanci na kungiyar Boko Haram da ISWAP.
Comments 1