Sarkin Yakin Yabo daya daga cikin masu ganin cewa tsohon Gwamnan Jahar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa Sen Aminu Waziri Tambuwal ya cancanci zama Shugaban marasa rinjaye a Majalisa ta Goma ta aka kaddamar
Ya bayyana dalilansa na ganin cewar kujerar shugaban marasa rinjaye na Majalisa ta goma bata wuce Sen Aminu Waziri Tambuwal ba
KARANTA NANAljanu Sun Yi Ram Da Wata Ɗalibar Makaranta Bayan Da Aka Jiyota Tana Sumbatu
Aminu Waziri Tambuwal sanannen mutum ne a harkar siyasa a Najeriya domin yayi aiyuka da dama kuma ya rike mukaman da duk wanda ya rike su baza a kirashi da yaro a siyasa ba
Tun lokacin da yana Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya Aminu ya nuna shi gogagge ne a siyasa har zuwa lokacin da ya zama gwamnan Jahar Sokoto a karkashin Jam’iyar APC kafin ya koma PDP
Ya jagoranci Sokoto tsawon shekaru 8 kuma yanzu ya zama Sanata,a karkashin inuwar PDP,Tambuwal ya nuna shi dan amana ne a PDP
Duk da kasancewar yana tsakiyar yan adawa hakan bai karye masa Gwuiwa ba inda ya jagoranci Kamfen na dan takarar PDP a babban zaben da ya gabata
Ina kyautata zaton cewar idan har Aminu ya zama Shugaban marasa rinjaye na Majalisa ta goma da zaa tabbatar a wannan makon,to ba zai ba PDP kunya ba
Zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya taimaka ma shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen gudanar da mulki cikin natsuwa da kwanciyar hankali domin ciyar da Najeriya gaba
A WANI LABARIN KUMA
Na Kagara In Dawo Cigaba Da Taka Leda-Sadiq Umar
Shahararren dan wasa gaba na tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad dake Sifen Sadiq Umar Ya Bayyana bukatarsa ta dawo wa don ya cigaba da taka leda
Sadiq ya shafe watanni yana jinyar raunin da ya ji a fafatawar su da kungiyar kwallon kafa ta Getafe a kasar Laliga