Wani tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Yerima, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya bukace shi da ya yi kokarin ganin an samu kwanciyar hankali a jihar ta Arewa maso Yamma da ‘yan bindiga suka daidaita.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Yerima wanda ya zanta da manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan ganawar sirri da Tinubu a ranar Litinin, ya ce nan ba da dadewa ba za a kawo karshen rikicin tare da sa baki a matsayinsa na Uba a jihar.
KARANTA WANNAN Shugabannin Hukumomin Tsaro Sun Gana A Zamfara
“Batun Zamfara, yanzu ni uba ne a jihar, mun yi mu’amala da Shugaban kasa da yammacin yau (Litinin) ya bukace Ni da na yi iya kokarina don ganin an samu zaman lafiya a jihar kuma abin da muke yi kenan.
Kuma da yardar Allah za mu taru za ku ga cewa duk rikice-rikicen da ke faruwa za su kare.” Inji Yerima.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke kai hare-hare akai-akai tare da yin garkuwa da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba domin neman kudin fansa.
Yerima wanda yayi gwamnan Zamfara daga watan Mayun 1999 zuwa Mayun 2007, kuma ya wakilci mazabar Zamfara ta yamma tsakanin watan Yunin 2007 zuwa Yunin 2019, ya ce hanya mafi dacewa da za a bi wajen magance matsalar ‘yan fashi da makami ita ce a fara tattaunawa.
Ya kara da cewa idan har tattaunawar ta gaza sannan gwamnati za ta iya tashi tsaye wajen ganin ta kawar da ‘yan fashin.
“Kuma ina ci gaba da cewa hanya mafi dacewa da za a bi wajen tunkarar matsalar ‘yan bindigar ita ce a fara tattaunawa amma kamar yadda na fada, idan har hakan ta gaza, gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen kawar da su.
“Dalilin da ya sa na ce ya kamata mu tattauna da su shi ne don guje wa barnar da za ta iya tasowa idan an dauki tsauraran matakai na aikin soja, wannan shi ne zabi na karshe,” in ji Yerima.
Sai dai wani kwararre kan harkokin tsaro, Bulama Bukarti, wanda ya kasance bako a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, ya ki amincewa da Yerima kan tattaunawa da ‘yan bindiga.
Burkati ya ce a maimakon haka ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da karfin soja wajen kawo karshen duk wani nau’in ta’addanci da ‘yan fashi.
A Wani Labarin Kuma Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Mashako
Cutar mashako wadda a turance ake ce mata (Diphtheria) cuta ce mai tsanani da nau’ikan kwayoyin cuta da ake kira Corynebacterium diphtheriae ke haifar da ke tokare magogwaro.
Tana iya haifar da wahalar numfashi, matsalolin bugun zuciya, har ma da janyo mutuwa.