Tsohuwar sarauniyar kyau ta Najeriya kuma mai bayar da tallafi, Tracy Solomon, ta ba da gudummawar kayayyakin ilimi ga makarantar sakandare ta gwamnati ta Mayo Dassa, dake Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Solomon, wanda ta samu sarautar kyau ta Najeriya a shekarar 2021, ta biya wa dalibai 20 kudin karatu, ta kuma ba da gudumawar jakunkuna da littattafan karatu sama da 1000 ga sauran dalibai.
Mai bayar da tallafin ta kuma bayar da kyautar jakunkuna na agajin gaggawa tare da kaddamar da filin wasan kwallon kafa a makarantar, a cewar Vanguard.
A yayin gabatar da jawabinta, ta ce, “Burina da jajircewata a matsayina na sarauniya da mai ba da taimako shine in sami damar taɓa rayuwa da kyau.”