By Abbas Yakubu Yaura
Masu aikin ceto a yankin kasar Comoros sun yi tururuwa domin gano wadanda suka tsira da rayukansu da kuma tarkacen jirgin da ke dauke da mutane 14 da ya yi hatsari a tsibirin Tekun Indiya a ranar Asabar.
Kamfanin Airline AB Aviation ya ce karamin jirginsa na Cessna ya bace daga Radar mai tazarar kilomita 2.5 (mil 1.6) daga inda ya nufa a lokacin da ya ke tafiya tsakanin Moroni babban birnin kasar da birnin Fomboni na tsibirin Moheli.
“Ayyukan bincike sun fara gano tarkacen jirgin a yankin gabar tekun Djoiezi da ke tabbatar da hatsarin,” in ji ma’aikatar sufuri ta Comorian a cikin wata sanarwa.
Gwamnatin Comoriya ta ce fasinjoji 12 ‘yan kasar Comoriya ne kuma matukan jirgin biyu ‘yan kasar Tanzaniya ne.
Hukumomi sun ce kwale-kwalen kamun kifi da aƙalla jirgin ruwa mai gudu ɗaya ne aka tura cikin gaggawa zuwa wurin da alamun siginal jirgin ya ɓace.
Ana ba da tallafi ga iyalai da abin ya shafa a tsibirin Moheli da Moroni na Grande Comore.
AFP