Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce tattaunawa tayi nisa da waɗanda su kai garkuwa da Fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.
Garba Shehu ya bayyana hakan a yau, ta cikin wani shirin siyasa na gidan talabijin Channels, wanda kuma Shehun ya kasance wanda aka tattauna da shi ta cikin shirin.
Yanzu haka dai a cewar sa sun samu rahoton cewa 9 daga cikin mutanen da akayi garkuwa da su sun mutu, yayin da 20 ke dauke da raunuka, tun bayan da aka yi garkuwa da su a watan Maris Yayin da suke hanyar komawa zuwa Kaduna daga Abuja.
Da aka tambaye shi kan shirin gwamnatin tarayya domin tabbatar da tsaro a bangaren jiragen kasan, Ya bayar da amsa da cewa wannan batun sirri ne daya danganci Tsaro, amma dai akwai shiri mai kyau.
Ya kuma ce ana ci gaba da samun fahimta tsakanin bata garin da kuma wadanda suka sace, domin ganin yadda zasu bayar da su ta ruwan sanyi.