Tawagar Kungiyar Gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin Gwamna Kayode Fayemi a ziyarar ta’aziyyar Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.
Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya John Kayode Fayemi ya jajantawa gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal bisa rasuwar yayansa Muhamamdu Bello.
Gwamna Fayemi ya ce ya je Sokoto ne a madadin takwarorinsa domin ta’aziyyar gwamnan kan alhinin mutuwar dan uwansa.
Gwamnan jihar Ekiti ya samu rakiyar takwaransa na jihar Edo Godwin Obaseki inda suka yi addu’ar Allah ya jikan marigayin.
Shi ma tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan jihar Sokoto bisa rasuwar babban yayansa.