Tsohon mataimakin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad, ya yi tsokaci kan wanda zai iya zama sabon ministan man fetur bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabbin ministocin kasar.
Ahmad yayi ikirarin cewa Tinubu ne zai cigaba da zama ministan albarkatun man fetur kamar dai yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a lokacin mulkinsa inda ya nada Tymipre Sylva a matsayin karamin ministan man fetur.
Ya yi nuni da cewa, Tinubu ya bi sahun tsofaffin shugabannin kasa, Olusegun Obasanjo da Buhari, wadanda suka zabi baiwa kansu ma’aikatar.
A wani rubutu da yayi a shafinsa na Twitter Ahmad ya rubuta cewa Shugaba Bola Tinubu ne babban ministan albarkatun man fetur na mu. Zai bi sahun tsofaffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari, wadanda suka rike mukamin a zamaninsu.
KARANTA NANYanzu Yanzu Gwamnoni Na Taron Gaggawa Da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima
A wannan karon akwai kananan ministoci guda biyu a karkashin ma’aikatar, karamin ministan mai da karamin ministan albarkatun iskar gas.
Tun da farko dai, DailyPost ta ruwaito cewa Tinubu ya gaza bayyana sunan ministan albarkatun man fetur yayin da yake nada mukaman ministoci a ranar Laraba.
A lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa kansa ma’aikatar tare da nada Timipre Sylva a matsayin karamin ministan man fetur.
Abinda wasu da dama a ciki da wajen kasar suka kira a matsayin wani mataki na rage almubazzaranci da kudaden gwamnati.
A WANI LABARIN KUMA
Muna Kyautata Zato Akan Sabon Ministan Noman Najeriya-Manoma
Kungiyar manoma a Najeriya ta bayyana cewar ta na matukar kyautata zaton cewar Sabin ministan albarkatun noma da Samar da Abinci da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Abubakar Kyari
Zai samar da yanayi mai kyau ga dubban manoma dake Najeriya yayinda bangaren Norman kasar ke gab da durkushewa sakamakon aiyukan ta’addanci a wasu yankunan karkara na kasar