Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Katsina ta tallafa ma Mutane 611
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da tallafin kayan gini ga Mutane 611 daga ƙananan hukumomi 7 da iftila’in ambaliyar Ruwa ya shafa a Jihar.
Hukumar da ke ba da agajin gaggawa ta Jihar Katsina SEMA ƙarƙashin Jagorancin Shugabar ta Hajiya Binta Hussaini Dan-gani ta bayar da tallafin a farfajiyar hukumar da ke Katsina.
Da yake ƙaddamar da bayar da tallafin, Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda wanda ya samu Wakilcin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Barista Mukhtar Aliyu Saulawa yace tallafin na a matsayin wani yunkurin Gwamnati na ganin ta rage ma al’umma raɗaɗin iftila’in da ya same su.
Gwamnan yayi kira ga al’umma da su guji zubar da shara a magudanan ruwa, saboda hakan na toshe ma ruwa hanya, inda yace hakan ke haddasa Ambaliyar Ruwan.
KARANTA WANNAN LABARIN:An Ragargaji Sojojin Najeriya A Niger, Har 36 Sun Riga Gidan Gaskiya
Daga nan Gwamnan ya jajanta masu akan iftila’in da ya same, Yana mai tabbar da ƙoƙarin Gwamnanatinsa na ganin ta tallafa ma al’umma a duk Lokacin da irin haka ta faru.
A nata Jawabin, Shugabar Hukumar SEMA ta Jihar Katsina Hajiya Binta Hussaini Dan-gani tace tun daga hawan Gwamnan kan kujerar sa hukumar ta bada tallafin kayayyaki da kudin su suka haura Naira miliyan 50.
Hajiya Binta Dan-gani ta ƙara da cewar, aikin hukumar ne bayar da irin wannan Tallafin musanman ga wadanda wani iftila’i ya sama, kuma hukumar na aiki tuƙuru domin ganin ta tallafa ma al’ummomin da wani iftila’i ya same su.
Daga nan sai tayi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su guji sayar da kayayyakin, tana mai jan hankalin su akan suyi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Daga cikin ƙananan hukumomin da suka amfana da Tallafin kayan ginin sun haɗa da karamar hukumar Katsina, da Funtua, Ɗandume, Daura, Mani, Charanchi, da kuma karamar hukumar Musawa.