- Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya bi sahun shugaban kasa mai barin gado, Muhammadu Buhari domin yin sallar Juma’a.
- An bayyana hakan ne a wata sanarwa da hadimin shugaban kasa mai jiran gado Abdulaziz Abdulaziz ya fitar a ranar 26 ga watan Mayu a Abuja.
- Buhari dai ya gayyaci tsohon gwamnan na Legas domin halartar taron addu’o’in da ya yi na karshe a masallacin fadar gwamnatin kasa
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar Juma’a da rana, ya bi sahun shugaban kasa mai barin gado, Muhammadu Buhari domin yin sallar Juma’a a masallacin gidan gwamnati, a ci gaba da shirye-shiryen bikin rantsar da shi,Punch ta rawaito.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da hadimin shugaban kasa mai jiran gado Abdulaziz Abdulaziz ya fitar a Abuja.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Jirgin Nigerian Air Ya Sauka a Abuja
Buhari dai ya gayyaci tsohon gwamnan na Legas ne domin halartar taron addu’o’in da ya yi na karshe a masallacin fadar gwamnatin shugaban kasa gabanin bikin rantsar da shi a ranar Litinin inda ake sa ran zai karbi bakansa na karshe daga ofis.
Daga cikin wadanda suka gudanar da sallar Juma’ar tare da su akwai tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun; Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, Janar Buba Marwa mai ritaya; Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mallam Garba Shehu, da wasu hadiman shugaban kasa.
A ranar Alhamis ne aka fara gudanar da bukukuwan mika mulki ga zababben shugaban kasa da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima tare da ba da lambar yabo mafi girma ta kasa tare da mika takardun bayanan gwamnatin Buhari ga shugaban kasa mai jiran gado.
Sanarwar ta kara da cewa, “An shirya gudanar da addu’o’in Musulmi da kuma hidimar Kirista a tsakanin mabiya addinai daban-daban a ranakun Juma’a da Lahadi.
“Yayin da aka ce za a gudanar da bukukuwan biyu a babban masallacin kasa da kuma cibiyar kula da lafiya ta kasa da ke Abuja, an kuma shirya gudanar da irin wannan taro a fadin kasar.
“Abubuwan za su kai ga cika ne a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu lokacin da tsohon gwamnan Legas aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa na 16 a tarayyar Najeriya.
“A wajen taron addu’o’in da ya samu halarta a babban masallacin kasa, zababben shugaban kasa, Tinubu ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa, Sanata Shettima.
“A duka masallatai biyu, Limamai sun yi addu’o’in samun nasara ga gwamnatin da ke tafe tare da rokon Allah Ya yi wa Tinubu da mataimakinsa jagorar tukin jirgin kasar zuwa wata manufa mai girma.
“Sun kuma gargadi Musulmi masu aminci da su ci gaba da tunawa da shugabanninsu da kasar nan a cikin addu’o’i kamar yadda Musulunci ya yi umarni.”
Da yake jawabi bayan kammala addu’o’in da aka gudanar a gidan gwamnatin kasa, Tinubu ya shaida wa manema labarai cewa ya zo ne domin ya hadu da shugaban kasa domin yin addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba shi goyon baya don gudanar da aikin gwamnati cikin nasara.
Zababben shugaban kasar ya kuma bayyana cewa zai sha ruwa daga mabubbugar ilimi da hikimar babban limamin masallacin fadar gwamnatin Kasa, Sheikh Abdulwahid Suleiman, wanda ya tunatar da ‘yan kasa kan nauyin amanar shugabanci.
A wani labarin kuma, Wani Manaja Ya Shiga Ha’ula’i Yayin Da Aka Gurfanar da Shi Gaban Kotu
An gurfanar da wani magidanci mai suna Damilola Isheniyi a gaban wata kotun majistare dake Abeokuta.
Gurfanar da manajan ya biyo bayan zarginsa da satar kayan aikin ma’aikata da kudi har naira miliyan 1.1.
An bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N100,000, tare da tsayayyun mutane biyu.