Yanzu haka dai jirgin saman Nigeria Air, ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja,Punch ta rawaito.
An ga jirgin yana motsi a cikin wani faifan bidiyo da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya wallafa a shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Jirgin Saman Nigerian Air Zai Fara Aiki Kafin Ranar Litinin – Sirika
Sirika ya rubuta, “Muna nan ga Allah madaukakin sarki. Hanya ce mai tsayi, mai ban gajiya, ban tsoro da wahala.
“Muna godiya ga kowa da kowa bisa wannan goyon baya. Wannan, da yardar Allah, zai kasance gare mu da kuma tsararraki masu zuwa.
“Ya Allah ka sa ya zama mai amfani ga kasarmu da al’ummarmu.”
A wani labarin kuma,Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP Ya Rattaba Hannu Kan Wata Doka
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde , ya rattaba hannu kan gyaran dokar sarakunan Gargajiya.
Makinde yana neman bai wa gwamna samun ikon cin gashin kansa don gabatar da nadin rawani ga sarakunan gargajiya a jihar.
Gwamnan yace “Kafin shigowata majalisar sarakunan gargajiya ba ta aiki, amma yanzu tana iya aiki.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Juma’a, ya rattaba hannu kan gyaran dokar sarakunan gargajiya a jihar, Cap.28.
Makinde yana neman bai wa gwamna samun ikon cin gashin kansa don gabatar da nadin rawani ga sarakunan gargajiya a jihar.