Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, a ranar Litinin din nan da rana, ya jagoranci taron kwamitin tsaro na kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayanin taron ba, majiyar jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa an kira taron ne domin duba halin da ake ciki na tsaro da kuma shugabannin hafsoshin su yi wa shugaba Tinubu bayani kafin ya tashi zuwa birnin New Delhi na kasar Indiya.
Taron an gudanar da shi ne gabanin zuwa dare ya tashi zuwa taron G-20 wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 9-10 ga Satumba.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito ceqa Taron na ranar Litinin wanda aka gudanar a dakin taro na shugaban kasar ya zo ne daidai watanni uku bayan da Tinubu ya kira taronsa na tsaro na farko da hafsoshin tsaro da suka yi ritaya. Wannan ne karo na uku tun hawansa kujerar mulkin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
KARANTA WANNAN Tinubu Ya Kalubalanci Hafsoshin Tsaro Da Cewa Akwai Babban Aiki a Gabansu
Wani rahoto na baya-bayan nan da kungiyar agaji ta Red Cross ta fitar ya bayyana ‘yan fashin da ke addabar yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a Najeriya a matsayin babbar matsalar tsaro a kasar.
Rahoton mai taken, Tambaya mai ma’anar: ‘Yan fashi da makami a yankin Arewa-maso-Yamma a Najeriya dangane da dokokin jin kai na kasa da kasa”
Ya ce ‘yan fashi da masu ta’addanci sun sanya Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma a kan gaba.
Ta ce yayin da ‘yan ta’adda suka kashe kusan mutane 350,000 tare da raba miliyoyi da muhallansu, asarar ayyukan ‘yan bindiga a wani lokaci ya zarce na ta’addancin Boko Haram.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Wadanda suka halarci taron tsaron sun hada da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa; Shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.
Ministan tsaro, Abubakar Badaru da karamin ministansa, Bello Mattawale sun halarci taron.
Babu wani daga cikin mahalarta taron da ya yarda ya yi magana da manema labarai har zuwa hada wannan rahoton.
A Wani Labarin Kuma Shugaban Karamar Hukuma Ya Samu ‘Yanci Daga Hannun DSS Da Ta Tsare Shi
Shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun, Honarabul Wale Adedayo, wanda hukumar tsaro ta farin kaya ta tsare shi tun ranar Juma’ar da ta gabata ya samu ‘yanci.
Adedayo, wanda ya zanta da wakilinmu a Abeokuta jim kadan bayan an sake shi, ya bayyana cewa hukumar DSS ta gayyace shi ne bisa wata takardar koke da aka rubuta a kansa na cewa yana yin kalaman tunzura jama’a da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.