Shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun, Honarabul Wale Adedayo, wanda hukumar tsaro ta farin kaya ta tsare shi tun ranar Juma’ar da ta gabata ya samu ‘yanci.
Adedayo, wanda ya zanta da wakilinmu a Abeokuta jim kadan bayan an sake shi, ya bayyana cewa hukumar DSS ta gayyace shi ne bisa wata takardar koke da aka rubuta a kansa na cewa yana yin kalaman tunzura jama’a da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Shugaban karamar hukumar da aka dakatar, ya ce ya shaidawa hukumar DSS cewa bai taba furta wata kalma ta tunzura jama’a ba face zargin da ya yi na cewa kananan hukumomi ba su da wani kaso daga gwamnatin jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata.
KARANTA WANNAN DSS Na Neman Damar Ci Gaba Da Tsare Emefiele A Hannunta
Ya ce ya zuwa yanzu bai firgita ba saboda halin da yake ciki, kuma ko shakka babu zai kalubalanci abin da ya kira dakatarwar da aka yi masa ba bisa ka’ida ba a ranar Alhamis din da ta gabata.
Adedayo ya bayyana cewa wasikar da aka rubuta an mika rahoton Gwamna Dapo Abiodun ga tsohon gwamnan jihar, Cif Olusegun Osoba, tare da goyon bayan wasu shugabannin jihar.
Amma ya ce ya yi mamakin yadda duk za su iya ficewa daga fafutuka tabbatar da kyakkyawan shugabanci tun daga tushe.
Idan dai ba a manta ba, shugaban da aka dakatar ya rubutawa wani tsohon gwamna a jihar Osoba wasika.
Inda kuma ya yi zargin cewa gwamnan jihar, Dapo Abiodun ya yi awon gaba da kudaden jama’a, yayin da kuma ya mika koken ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a kan wannan zargi.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Kwamitin hada-hadar kudi da rabon kudi a jihar mai alhakin kula da kason kudaden kananan hukumomin tarayya ya yi watsi da wannan zargi, tare da tabbatar da cewa duk wani asusu da kwamitin ya amince da shi ya bi ta asusun kananan hukumomi daban-daban.
A Wani Labarin Kuma FG Ta Roki Kungiyar Kwadago Da Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gargadin
Gwamnatin tarayya ta roki shugabannin kungiyar kwadago ta Kasa da su janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka shirya farawa ranar Talata.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ne ya yi wannan roko a ranar Litinin din nan a Abuja.