Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dokokin kasar, Smart Adeyemi ya ce shugaba Bola Tinubu zai kori duk ministar da ya kasa yin aiki nan da watanni shida.
Adeyemi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba.
Ya ce abin da ya kamata ‘yan Najeriya su sani game da shugaban kasa Bola Tinubu a yau, ciki har da wadanda suke ministoci, shi ne, daga tarihinsa, da zarar kayi wata shida baka nuna alamun aiki ba sai ya nuna maka mafita.
Abin da zai yi ke nan Tinubu yana gaggawar kawo canji. Asiwaju yana son yin suna. Yana so ya mayar da Najeriya. Yana so ya maido da kasar cikin hayyacinta.
Karanta nanTinubu Ya Ce Mu Tantance Olukoyode Duk Da Bai Cika Ka’ida Ba-Majalisar Dattawa
Ina taya wadanda suka samu mukaman ministoci murna amma ku sanibcewa matukar kuka kasa yin abinda ya dace nan da wata shida Tinubu zai koreku.
A halin da ake ciki, Adeyemi ya ce abubuwan da shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima suka samu a majalisa, zai taimaka musu wajen yin kyakkyawan aiki.
Adeyemi, wanda kuma dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne a zaben gwamnan Kogi ya lura cewa, da zarar wani ya kasance a majalisar dattawa, mutumin ba zai iya gazawa ba.
Ya ce wannan shi ne karo na farko da muke samun ‘yan siyasa masu rike da madafun iko na gwamnati.
Shugaba Bola Tinubu, tsohon Sanata; Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, tsohon sanata, har ma da uwargidan shugaban kasa, Mrs Oluremi Tinubu sanata ce.
A wani labarin kumaRaina Ne Ya Baci-Sen Abbo Ya Baiwa Akpabio Hakuri Akan Kalamansa
Idan ka duba jihohin da tsofaffin Sanatoci ke mulki za ka ga kwazon aiki kamar Hope Uzodubma na jihar Imo.
Adeyemi ya ce gwamnatin Tinubu za ta farfado da dimbin ayyukan tattalin arziki da fa’ida a kasar nan tare da samar da damammaki na ci gaban tattalin arziki na gaske.
Ba zai baku aiki ba bisa kabila ko addininku, yana la’akari da ingancin tunanin ku, da yadda hankalinku yake aiki.