Wike ya yi wasu kalamai kan kafa wasu dokoki da suka sabawa addinin Musulunci
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi watsi da ikirari na adawa da tsarin addinin Musulunci a Najeriya.
Wike ya ce gwamnatinsa ba ta yin “dokokin da suka sabawa tsarin Musulunci.”
KARANTA WANNAN LABARIN:Filin Jirgi: Gwamnan Ya Nuna Ɓacin Ransa Kan Rashin Gudanar Da Aiki Mai Nagarta
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na masallacin Abuja na kasa karkashin jagorancin shugaban su, mai martaba Alhaji Yahaya Abubakar, Etsu na Nupe.
Ministan ya ce mutanen da ke kokarin tayar da hankulan addini suna yin hakan ne da mugun nufi domin samun matsayi a siyasa.
A cewar Wike, “A Najeriya, ba ni da wani dalili na tayar da kiyayya ga wata kungiya ta addini, a maimakon haka ya kamata in goyi bayan duk wanda ke fafutukar neman alfarma.”
Sai dai ya ba da tabbacin cewa FCT zata yi gaggawar tallafa wa tare da kula da Masallacin kasa, da Cibiyar Kula da Lafiyar Jama’a, kasancewar an ayyana shi a matsayin abin tarihi na kasa, ya kuma yi kira ga malaman addini da su yi wa’azin hadin kan kasa da zaman lafiya.
“Babu wata gwamnati da za ta yi kasa a gwiwa wajen tallafa wa wani abin tunawa na kasa, na Kirista ko Musulmi.”
Shi ma da yake jawabi, Etsu Nupe ya bukaci Ministan da ya tallafa wa aikin kula da Masallacin na kasa, wanda ya bayyana cewa an dade da dakatar da shi.
A wani labarin kuma:Tinubu ya amince da buɗe jami’o’i biyu da aka kafa a zamanin Buhari
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da fara ayyukan ilimi na sabbin jami’o’i shida cikin 14 da aka kafa a kwanakin karshe na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ministan Ilimi Tahir Mamman ne ya bayyana haka a ranar Laraba, bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaba Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja.