Wani mutum ɗan Najeriya ya bayyana yadda auren ɗan’uwan sa ya samu tsaiko a dalilin kuɗin sadaki.
Lamarin ya auku ne a jihar Imo a yankin Kudu maso Gabas, na Najeriya inda aka samu tsaiko a dalilin doyar da aka kawo matsayin kuɗin sadaki. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Wata tsohuwa ta samu kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan an sanya a rawar TikTok
Wani mai amfani da @Foedosa1 a manhajar Twitter shine ya bayyana hakan yayin da yake martani kan wata magani da wani mai faɗa aji yayi a Twitter inda yake cewa jihar Edo itace jihar da ta fi kowace jiha arhar sadaki.
A cewar @Foedosa1, surukan ɗan’uwan sa sun sanya a kawo doya guda 400 a cikin kuɗin sadakin. Sai dai akan hanyar su ta zuwa ƙauyen domin kai doyar, ɗaya daga ciki ta karye.
Kamar da wasa iyayen amaryar suka ƙi amsar ragowar doyar, inda suka haƙiƙance cewa sai an je kasuwar ƙauyen an sauya wacce ta karye.
Dalilin su kawai shine ƙafar amaryar lafiyar ta ƙalau bata karye ba.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su akan wannan lamarin, ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@TabithaOkenwa ta rubuta:
“Amma na sha tambayar kai na wannan tambayar ita kaɗai duk lokacin da na gani ko naji irin wannan abun ya faru. Tambayar itace me zasu yi da doya 400. Ko suna shirin sake sayar da ita ne ko kuma me? Na rantse da nice amaryar sai nayi wannan tambayar.”
@ayinla_mayowa1 ya rubuta:
“Dama ina son nayi wannan tambayar, meyasa wasu iyayen suke yin haka? Shin suna yin hakan ne domin su sanya wanda zai auri ƴar su ya sha baƙar wuya ko kuwa son tsabar haɗama ce domim ganin sun ƙarar masa da ɗan abinda yake aljihun sa?”
Gwamnatin Binuwai Ta Kaddamar Da Titin Guma Mai Tsawon Kilomita 30.5, Ta Gyara Babban Asibitin Garin
A wani labarin na daban kuma, gwamnatin jihar Benuwai ta ƙaddamar da wani aikin babban titi da gyaran asibiti.
Gwamnatin jihar Benue ta kaddamar da aikin titin Gbajimba-Tse-Ortom zuwa Tse-Upev-Tse-Akaahena mai tsawon kilomita 30.5 a karamar hukumar Guma, wadda gwamnatin Gwamna Samuel Ortom ta gina.
Haka kuma an ba da aikin yi wa babban asibitin Gbajimba da ke karamar hukumar Guma gyara.