Wani Matuƙin Babur wanda har yanzu ba’a gano shi ba, a ranar Juma’a ya mutu akan hanya, biyo bayan hatsarin daya afku a Gbongan ta Jahar Osun.
Marigayin dai yana tafiya akan Babbar hanyar Gbongan-Ile-Ife, an ruwaito cewar yayi kuskuren gittawa wata Tirela, wanda ya haddasa murƙushe shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Dalibin Shekarar Karshe Na Jami’ar BUK Ya Rasu A Dakunan kwanan dalibai
Mutane biyu da hatsarin ya rutsa dasu basu ji raunuka ba.
Mai Magana da Yawun Hukumar Kula da hanyoyi ta Ƙasa reshen Osun Agnes Ogbungbemi a lokacin da yake magantawa, yace hatsarin ya afku da misalin ƙarfe 4.40pm.
“Hatsarin ya afku akan hanyar Gbongan-Ile-Ife. Ya afku ne sabudda kuskuren wuce motar. Ya faru ne tsakanin Tirela ƙirar Iveco Eurostar da Babur Jincheng.
“Iyalan marigayin sun ɗauki gawar mutumen, yayinda ƴan sanda suka tafi da Motar,” inji Ogbungbemi.