‘Yar wasan Najeriya Tobi Amusan ta lashe gasar tseren mita 100 na mata a gasar Diamond League da ke Zurich ranar Alhamis din nan.
Ta kammala a dakika 12.29 don kare kambunta na gasar Diamond League. Tia Jones daga Amurka ta biye mata baya inda ta zo a dakika 12.40s yayin da Britany Anderson ta Jamaica ta zo ta uku.
Yar Najeriyar dai ta lashe kofin gasar Diamond League a bara cikin dakika 12.42. Ta kuma kafa tarihi a Afirka.
“Tobi Amusan ta kare kambunta na gasar DiamondLeague tare da sabon tarihin haduwa a tseren mita 100 na mata!”
Karanta kuma: Buhari Ya Taya Yar Wasan Tseren Najeriya Murnar Lashe Zinare
A watan Yuli, ta zama ‘yar Najeriya ta farko da ta lashe zinare a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya. Ta yi nasara a tseren mita 100 na mata a Eugene, Oregon, wadda ta kare kambun a cikin dakika 12.06 mai ban mamaki.
A yayin wasan kusa da na karshe na gasar, Amusan ta yi gudun dakika 12.12 don karya tarihin duniya a filin Hayward.
Amma ba a san lokacin da ta yi nasara a matsayin tarihin duniya ba saboda iskar da ta kada na mita 2.5 a cikin dakika daya.
Makonni kadan a gasar Commonwealth, Amusan ta sake lashe lambar zinare a tarihin Najeriya. Ta ci karo da sabon tarihin wasanni na dakika 12.30 don ci gaba da gasar tseren mita 100 da ta yi nasara a shekaru hudu da suka gabata a Gold Coast, a Australia.
Gidan talabijin na channels ta rawaito cewa, A wannan watan, ta zo na biyu a tseren mita 100 na mata a gasar wasannin Diamond League ta Athletissima a Lausanne, ta Switzerland.
Jasmine Camacho-Quinn ta Puerto Rica wacce ta yi tseren dakika 12.34 a gasar ta doke zakaran duniya kuma mai rike da kambun duniya zuwa matsayi na farko.
A wani labarin kuma: Zanga-zanga: NANS Ta Yi Kira Da A Gaggauta Sasanta Yajin Aikin ASUU
Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi kira da a gaggauta warware yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, Zababben shugaban kungiyar NANS Umar Faruq-Lawal ne ya yi wannan kiran a Abuja yayin da yake jawabi ga manema labarai kan ci gaban yajin aikin na ASUU.