Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya koka kan tsadar man dizal, inda ya ce tsadar da yayi na dagula harkokin kasuwancinsa.
Obasanjo wanda kuma ya kasance manomin kifi ne ya ce yana fama da shan zufa ne saboda tsadar man dizal.
Ya yi magana ne a ranar Talata a Abeokuta, dake Jihar Ogun, yayin taron manoman kifi na Kudu maso Yamma da aka gudanar a dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL).
Tsohon shugaban kasar ya yi nuni da cewa hauhawar farashin man dizal da kuma hauhawar farashin kifin da ake samu akai-akai zai sa manoman Najeriya su daina kasuwanci.
Amma a cewarsa sai dai idan sun hadu aka amince da farashi mai dorewa da za a amince da shi don ci gaba da kasuwanci, bayan an kara farashin ga masu siye.
A cewarsa, manoma za su iya kara yawan abinda suke samarwa, bisa tausayin masu saye da za su zo a kowane irin adadin da ya dace da su ba tare da la’akari da illar da tattalin arzikin da ake samu a halin yanzu ke haifar da samar da irin wadannan kifi ba.
Ya bayyana cewa a halin yanzu farashin dizal a kan lita daya yana kaiwa Naira 800, kuma ana samar da kilo daya na kifi Naira 1,400, inda ya kara da cewa, domin samun riba kadan, manoma ba za su iya sayar da kasa da Naira 1,500 akan kowane kilo ba, kuma wannan yana nufin “asara kai tsaye.”
Obasanjo ya ce “Farashin man dizel ya yi tsada saboda yadda ake tafiyar da kasar nan ba haka ya kamata a tafiyar da ita ba.
Bayan haka, abin da zai faru shi ne, musamman mu da za mu yi amfani da dan dizal wajen samar da kifi, gaba daya za mu shiga talauci, kuma idan hakan ta faru, ‘yan Nijeriya za su ci gaba da cin kifi.
A don haka ne ya bukaci gwamnatin tarayya, daukar matakan daya kamata, don kawo karshen tsadar man.