Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rushe wani haramtaccen gini a gaban gidan Sheikh Nasiru Kabara cikin gaggawa.
Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin hakan bayan bincike ya nuna cewa ba a taba bayar da izini a hukumance ba kan ginin walau daga Gwamnati ko Masarautar Kano.
Hon. Baffa Babba Ɗan’agundi, shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA, wanda ya zama shugaban kwamitin kawar da haramtattun gine-gine shine ta sanar da hakan a wata Sanarwa da aka tanada manema labarai ta hannun mai magana da yawun hukumar Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa.
”Yana da kyau jama’a su sani cewa wannan haramtaccen ginin ya janyo cece-kuce tsakanin gwamnatin jihar da Masarautar wanda duk da cewa dayan bangaren na da hannu a ciki amma bayan da aka yi bincike aka gano cewa wasu masu son zuciya da son rai ne kawai suka shige gaba wajen aiwatar da hakan.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Gwamna Ganduje ya bayar da umarnin rushe gaba daya, ginin shagunan da aka fara.
A don haka za a ci gaba da barin wajen ga kungiyar Kadariyya da ke amfani da shi wajen yin zikirin.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a samar da jami’an tsaro 24/7 a yankin domin kare matasan da kan yi amfani da filin wajen wasanni kala kala.