Ga dukkan alamu ’yan takarar shugabancin }asar nan a zaben 2019 za su fara fafata ya}in neman zabe gadan-gadan. Koda ya ke sai dai a ce za su }addamar, domin dukkan su sun fara ya}in ko dai a fakaice, ko a }ar}ashin }asa ko kuma ta yadda ‘yan Najeriya ke ta bayyana ra’ayoyin su a kafafen ya]a labarai, soshiyal midiya, wuraren taruka, fastoci, majalisin matasa da na dattawa a unguwanni, tashoshin mota har ma da teburan mai shayi.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta }asa (INEC) ce ta bayar da iznin a fara gudanar da kamfen daga ranar Lahadi, 18 Ga Nuwamba, 2018. Amma wannan izni ya na kan masu takarar shugaban }asa ne da kuma majalisar tarayya ka]ai.
Sama da jam’iyyu 50 ne suka shiga takarar shugaban }asa, amma an maida hankali ne kacokan a kan jam’iyyar APC mai ri}e da mulki da kuma PDP, babbar jam’iyya mai adawa. Ana sa ran cewa daga cikin wa]annan jam’iyu biyu ne shugaban }asa zai fito. Ko dai Muhammadu Buhari dan takarar APC, wanda ke kan mulki a yanzu, ko kuma tsohon Mataimakain Shugaban }asa, Atiku Abubakar na PDP.
KO GUGUWAR BUHARIYYA ZA TA SAKE YI WA PDP |ARNA?
Bisa dukkan alamu fitowar Atiku ]an takarar jam’iyyar PDP ta girgiza jam’iyyar APC da magoya bayan ta. A kullum cewa su ke yi mummunan kaye za a yi wa Atiku a zabe, amma kuma a gefe ]aya APC da magoya bayan ta, ba su da wani aiki sai kamfen na ya}i da Atiku a soshiyal midiya da sauran kafafe.
Zai yi wahala jam’iyyar APC ta samu irin gagarimin goyon bayan da ta samu a fa]in }asar nan kamar yadda ta samu a zaben 2015. Shekaru kusan hu]u bayan APC ta hau mulki, jam’iyyar ta ha]u da matsaloli, cikas, rikice-rikice da kuma rigingimun zaben shugabannin jam’iyya na kananan hukumomi, jihohi da tarayya, wa]anda aka ha}i}ance an tafka son kai sosai. Wannan ya janyo wa jam’iyyar cikas.
Ficewar-farin-]ango da aka ri}a yi a cikin APC ana komawa PDP da sauran jam’iyyu, musamman PDP a Majalisar Tarayya, ya haifar wa APC koma baya matu}a. Da yawan sanatoci da mambobin tarayya sun fice, wasu sun koma PDP jam’iyyar su ta asali, wasu kuma sun shiga wasu jam’iyyu.
Zarge-zargen za~en-fidda-gwani a tsakanin APC ya karya darajar jam’iyyar. Da dama wa]anda aka yi wa ba daidai ba, ba za su maida hankalin su da magoya bayan su su yi wa jam’iyya kamfen ko su zabi APC ba.
Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshimhole na ta gaganiyar fitar da kan sa daga zargin kar~ar ma}udan ku]a]en da ya yi sanadiyyar dagulawa da baddala za~ukan fidda-gwani na APC a fa]in }asar nan.
Har yanzu akwai gwamnoni da dama wa]anda za~en-fidda-gwani bai musu da]i ba, kuma suna kan rikici da shugaban na jam’iyyar APC.
Akwai rigingimu da shari’u masu ]imbin yawa kwance a kotu, wa]anda hasalallun jam’iyyar APC suka kai }ara, tun bayan kammala za~en fidda-gwani. Jihar Rivers da kuma Imo na daga cikin inda rigingimu suka fi tsamari a kotu.
Tuni dama INEC ta hana APC shiga za~en 2019 a jihar Zamfara, saboda rigingimun da suka tirni}e a jihar har za~en fidda-gwani ya gagara a kan lokaci.
Tulin wa]anda suka goya wa Buhari baya a za~en 2019 sun dawo daga rakiyar sa ko rakiyar jam’iyyar sa. Da yawan su sun zuba ido a yanzu, wasu kuma sun sauya sheka.
Shi kan sa kishin ‘Buhariyya’ ]in da ake yi, bai kai zafin na 2015 ba. Da dama wa]anda suka yi Buhariyya bakin rai bakin fama a baya, yanzu sun watsar da a}idar.
Matsalolin da wasu gwamnoni musamman a Arewa suka haifar wa mulkin Buhari, zai bai wa APC cikas a za~en shugaban }asa.
An bada }ofa ‘yan takara da dama sun kashe ku]a]e sun sayi fam na takara, kuma sun kashe ma}udan ku]a]e wajen kamfen na za~en fidda-gwani, amma daga baya an yi musu magu]i, wasu kuma an maye gurbin su da wa]anda ko ma kamfen ba su fita sun yi ba.
MATSALAR SALON MULKIN BUHARI
Irin yadda Buhari ke tafiyar da mulkin sa, bai yi daidai da yadda jama’a suka yi tunanin zai yi ba idan ya hau mulki. Akwai da dama masu ganin cewa tafiyar mulkin Buhari a karkace ta ke, kuma a daburce.
YA{I DA CIN HANCI DA RASHAWA da mulkin Buharin ke tutiya da shi, ya na samun cikas ko kuma kakkausar suka daga jam’iyyar adawa da kuma masu sharhin al’amurran yau da kullum. Ana ganin bi-ta-da-kulli ya fi yawa a ya}i da cin hanci.
An fi karkata da maida hankali wajen takura masu adawa a batun ya}i da cin hanci, a gefe guda kuma an kyale na jikin gwamnatin Buhari. Irin su Rotimi Amaechi, Adam Oshimhole, Bachir Lawan, tsoffin jami’an NIA, SSS, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban }asa Babachir Lawal, duk akwai alamomin tambaya a kan su.
Kusan shekara hu]u kenan Buhari na ya}i da cin hanci da rashawa, amma tsoffin gwamnoni biyu ka]ai ne aka ]aure, wato Jolly Nyame da Joshua Dariye. Su ]in ma ba gwamnatin Buhari ce ta gurfanar da su a kotu ba. Tsohuwar shari’a ce da ta gada.
Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Godswill Akpabio, wanda EFCC ke neman naira Bilyan 117 a hannun sa, a kwanan baya Shugaba Buhari ya yi masa kyakkayawar kar~a zuwa APC, a daidai lokacin da ake ta tafka shari’ar wasu ‘yan PDP da ake tuhuma da wawurar ku]a]en da wasu ma ba su kai naira Bilyan 1 ba.
ASUSUN BAI [AYA (TSA) da Gwamnatin Buhari ta shigo da shi, bai hana satar bilyoyin ku]a]e a }ar}ashin mulkin Buhari ba. A kullum ana buga labaran har}alla, cuwa-cuwa da karkatar da bilyoyin ku]a]e da jami’an gwamnatin Buhari ke yi. Fallasa Gwamna Ganduje, kama wasu ministocin Buhari da takardun jabu, kama shugaban Hukumar Kula da Kafafen Ya]a Labarai, Ishaq Kawu da wuru-wurun naira bilyan 2.5 ba karamin cikas ba ne ga gwamnatin Buhari.
MATSALAR TSARO sai }ara munana ta ke yi a Arewacin }asar nan. Duk da cewa Boko Haram sun daina fantsama a kai hare-hare a sauran jihohin Arewa, har yau a Jihar Barno sai }ara }arfi suke yi. Haka kuma sai hare-hare suke }ara }aimin kaiwa a garuruwa, }auyuka kuma gadan-gadan a kan sansanin sojoji. Babu alamar cewa za a iya kakka~e su nan da ‘yan shekaru ka]an masu zuwa.
GARKUWA DA MUTANE a jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da wasu garuruwa ya yi munin da kusan a rana tsaka ana gani aka sace mutane 40 ko ma fiye, musamman a tsakanin yankin Birnin Gwari da jihar Zamfara.
JA-IN-JA KAN {ARIN ALBASHI da ake ta yi domin ganin an kai mafi }an}antar albashi ya koma naira 30,000, shi ma babbar matsala ce, domin har ma’aikata sun fara barazanar cewa ko a }ara musu ko kuma su yi gaba da Buhari a zaben 2019.
’Yan Arewa da dama na }orafin rashin aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a jihohin Arewa, musamman a Sokoto, Zamfara, Katsina, Jigawa da Kano inda Buhari ya samu kuri’u masu tarin yawa.
TATTALIN ARZ{IN {ASAR NAN da ake cewa ya na farfa]owa, cike ya ke da sar}a}iya, kasancewa kusan yanzu albashin ma’aikata ne ka]ai gwamnati ke iya biya da ku]a]en ribar man fetur da ake rabawa a duk }arshen wata. Sauran manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa na }asafin ku]a]e, duk da ku]in bashi da lamuni daga }asashen waje ake gudanar da ayyukan.
FA[UWAR DARAJAR NAIRA har yau ta }i sauka ko da }asa da naira 300 a madadin Dalar Amurka ]aya. Naira ]aya ta haura fam 400 na Ingila, kuma ta na daidai da Dalar Amurka 360. A kan wannan lissafin ne ake ta ciwo wa Najeriya bashin da babu yadda za a yi }asashen da ke bayar da bashin su yarda darajar Dala, Fam na Ingila da Yuro su karye har naira ta yi daraja.
JUMA’AR BUHARI TA FARA DAGA LARABA: A kullum Buhari na shan alwashin cewa gwamnatin sa ba za ta yi katsalandan a al’amurran za~en 2019 ba. Da dama sun gamsu da kalaman sa. Da yawa kuma ba su gamsu ba, saboda sun auna sun ga yadda aka tafka magu]i a za~en shugabannin APC na }ananan hukumomi da jihohi. Buhari bai yi komai ba, sai dai cewa ya yi wa]an]a aka kayar su hakura.
Haka ta faru a za~ukan-fidda-gwanin APC a }asa baki ]aya, zargin tafka magu]i ya farra}a jam’iyyar APC matu}a. A kullum sai rigingimu ke }ara kunno kai, bayan kuma wasu na kotu a gurfane. Bayan kammala za~en sai Buhari ya ce wa]an]a aka yi wa rashin adalci su hakura, ko kuma idan abin ya yi maka ciwo, ka tafi kotu mana. Wannan kalami na sa ya ba}anta wa da dama rai.
ZA|UKAN EKITI DA OSUN an samo ‘yan matsaloli ta yadda har ita kan ta INEC ta koka da yadda jami’an tsaro suka ri}a cin zarafin masu ka]a kuri’a daga ~angaren masu adawa da kuma ‘yan jarida. Har yau gwamnatin Buhari ba ta yi komai a kai ba.
ATIKU: KADA MAGE BA YANKA BA
A can baya Atiku Abubakar ya sha fitowa takara, amma dai a wannan karo na hu]u ne ake ganin zai fi yin takarar bakin rai bakin fama. Ko a ce sai inda mai ya }are, ko sai inda }arfi ya }are, ko kuma sai inda ku]i ya }are. Ba APC ko Buhari ko kuma kowane ]an Najeriya ba, duk duniyar da ke bibiyar siyasar Najeriya ma an san a wannan karon Atiku da gaske ya ke yi. Idan ya yi nasara, to PDP ta sake kar~e mulki kenan. Idan kuma ya sha }asa, to an yi masa kayen-bankwana-da-siyasa kenan.
Atiku ya na da goyon bayan kusan sauran ‘yan takarar da ya kayar a za~en fidda-gwani. Wasun su da dama ma su na cikin tawagar kamfen ]in sa da a ka fara }addamarwa a ranar Litinin.
Ba}in fentin da PDP ta yi wanka da shi a lokacin gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan, musamman zargin kwashe ku]a]en da aka yi kamfen da su a 2015, har yanzu bai gama kankaruwa daga fatar jikin jam’iyyar ba.
Da dama manyan jam’iyyar wa]an]a suka taka rawa a lokacin gwamnatin Jonathan wasu ba su }asar, wasu kuma sun yi shiru ba su magana.
Bisa dukkan alamu har yau Atiku bai ]auki darasi ba daga za~ukan da ya ta~a fitowa takara a baya ba. Gaba ]aya harkokin kamfen ]in Atiku sun fi karkata ne a hannun ‘yan kudancin }asar nan. Tafiyar kamfen ]in Atiku da ya]a manufofin sa, ba ta cika bayar da muhimmanci a ~angaren Arewacin }asar nan ba, musamman ma cikin Hausawa ko kuma bai wa harshen Hausa muhimmanci, a yankin da Buhari ya fi magoya baya.
ATIKU: KAI KA[AI GAYYA: Kusan a iya cewa Atiku Abubakar ne babbar gayya a cikin jam’iyyar PDP. Shi ne uwa kuma shi ne uba, sannan kuma shi ne mai hannu da shunin da zai bai wa kowa murjin zare. Duk wani mai }arfi a cikin PDP, to bayan Atiku ya ke.
MARTANIN ATIKU KAN ZARGE-ZARGEN SA:
Matsalar ‘yan Nijeriya ita ce, su a tunanin su, mutum ba zai iya gina kan sa ba, sai ya ha]a da ku]in sata.
Abin bacin rai ne a ri}a amayar da zargin sata a kai na, alhali an kasa fitowa da hujja ko da guda ]aya wadda ta tabbatar da cewa na wawuri dukiya a lokacin da na ke aiki.
Mutane masu dakusassar kwakwalwar rashin tunanin }ir}iro dabarun kasuwanci, su a ko yaushe gani su ke yi kowa ma ~arawo ne kamar su.
Idan har Atiku ~arawo ne saboda kallon irin ]imbin kasuwancin da ya ke yi da dukiyar sa, to ina so abokan gabar siyasa ta su fito su shaida wa ‘yan Nijeriya su na su hanyoyin da su ka bi su ka mallaki ]imbin dukiyar da suke da ita.
Ina }alubalantar duk wani wanda ke da wata hujja ko hujjoji cewa na wawuri dukiyar }asar nan, to kada ya rufa min asiri, ya fito ya tona ni.
Idan na zama shugaban }asa, ina da tabbacin cewa zan bai wa kowa mamaki, saboda na yi imani cewa zan yi ya}i da cin hanci da rashawa fiye da yadda kowa ma ya taba yi a baya.
Duk da ma}ar}ashiya da algungumancin da ake kitsawa don a danganta ni da har}allar William Jefferson a Amurka, an yi shari’ar kuma an kammala tun a 2009, amma ba a kama ni da laifin komai ba.
{A{A TSARA {A{A
Daga yau dai saura ‘yan kwanaki a gudanar da za~en shugaban }asa. Abubuwan da za su biyo baya a cikin wa]annan kwanaki, sun ha]a da rangadi, hayaniya, kamfen, ambaliyar fastoci da hotuna, tumbatsar marubuta, kalaman adawa a kafafen ya]a labarai, tuggu da algungumanci da kuma dandazon taro da zugar masu ya}in neman za~e.
Tun daga yanzu har zuwa ranar 16 Ga Fabrairu, 2019, babu sauran barci mai nauyi a idanun wasu, har sai bayan sun yi nasara, ko kuma bayan sun sha kaye.