Tun lokacin da gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Majalisar Dokokin jihar da kuma fadar gwamnatin jihar da ke karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje su ka ayyana aniyarsu ta tsittsinka masarautar Kano da gididdibata zuwa kashi biyar a ke ta samun ra’ayoyi daban-daban kan wannan mataki da gwamnatin ta dauka kimanin makonni biyu da su ka gabata. Babban abinda mafi rinjayen masu bayyana ra’ayi su ka fi yin amanna da shi shi ne, wannan matakin ba za a iya raba shi da badakalar siyasa ba, inda dangantaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Ganduje da Mai Martaba Amir Kano Muhammadu Sanusi II. Wasu na ganin cewa, azabar da gwamnan ya sha wajen kokarin zarcewa a mulki, inda ya kai labari da kyar da jibin goshi a zagaye karo na biyu, sarkin na da hannu a ciki la’alla ko dai ya yake shi ta karkashin kasa ko kuma ya ki yarda ya dafa ma sa ta yadda zai iya zarcewa cikin sauki ba tare da tayar da jijiyar wuya ba ballantana har kima da darajar gwamnan da gwamnatin tasa su yi faduwar bakar tasa irin yadda a ka gani a lokacin zaben gwamnoni na 2019 da a ka gudanar ranar 9 ga Maris, sannan a ka gudanar da zagaye na biyu ranar 23 ga watan na Maris bayan da Ganduje ya kusan shan kayi a zagayen farkon. Wasu na ganin cewa, a kokarin Ganduje na daukar fansa ne ya sanya a ka dawo da bincikar kashe kudi na fadar sarkin, sannan kuma kirkiro sababbin masarautu a jihar hanyar yanke fadin fada-a-jin sarkin, inda ya bar shi da kananan hukumomin birni da kewaye kawai a karkashin kulawarsa. Gwamnatin jihar dai ta kirkiro masarautun Bichi, Gaya, Karaye da Rano ne a wannan sabon tsarin, sannan kuma ba ta bar wa Kano ikon shugabantar majalisar sarakuna ta jihar ia kadai ba, kamar yadda a ka saba yi a jihohin da su ke da sarki mai daraja ta daya fiye da guda, inda sabuwar dokar ta ce, za a rika yin karba-karba ne, akamr mulkin siyasa, duk bayan shekara biyu, amma gwamna ya na da ikon yiwa shugaban majalisar mai ci tazarce a karo na biyu kurum; abinda a ke gani a matsayin kaskanta masarautar da ta ke da dimbin tarihi da kwarjini ba a Najeriya kadai ba, har ma a Afrika da duniya bakidaya. Wadannan abubuwa da su ka faru akwai masu ra’ayin cewa, maimakon Gwamna Ganduje ya huce haushinsa a kan bakidayan masarautar, wacce watarana da shi Gwamna Gandujen da Amir Kano Sanusi din za ya cigaba da kasancewa har bayansu, me zai hana ya huce haushinsa kan sarkin kadai ta hanyar yi ma sa bi-ta-da-kulli wajen haifar da tafalilin tunbuke shi, kamar yadda ya faru ga kakansa da ya gada, Muhammadu Sanusi na Daya? Du ka da cewa, akwai masu ganin wannan ma ba dabara ba ce, domin a na ganin cewa, Sarki Sanusi wani kusa ne a duniya, wanda zai iya amfanar jihar, saboda kimar da ya ke da ita a idanun kasashen duniya, ba wai Najeriya kadai ba. Sai dai kuma akwai masu ganin cewa, tsige sarkin zai fi alheri, domin hakan zai hana sarakuna a nan gaba tsoma hannu a harkokin siyasa da kawo cikas ga ’yan siyasar.