Gidan Talabijin na Channels sun labaro cewa wasu daga cikin tsofin sojojin Nijeriya na zanga-zanga a gaban hedikwatar ma’aikatar kuɗi ta ƙasar da ke Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa tsofaffin sojojin na zanga-zangar ne sakamakon ƙin biyansu haƙƙoƙinsu da ba a yi ba.
Sojojin na kira ga gwamnatin ƙasar da ta amince ta biya su kuɗin da suke bi tun daga 2019 zuwa yanzu.
Haka kuma, suna buƙatar a dakatar da zabge kuɗaɗen fansho na duka malaman kiwon lafiya na soji da kuma saka sojojin da suka yi yaƙin basasa a cikin tsarin na fansho.