Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Argentina wanda ya fafata wasanni a manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na nahiyar Turai dama yankin kudancin Amurka, inda daga cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan daya fafatawa wasa akwai Manchester United da kuma Juventus na ƙasar Italiya wato Carlos Tevez ya bayyana wata magana dangane da rataye takalmansa.
Mafi yawan ‘yan wasa suna jingine takalmansu a ƙasarsu ta haihuwa da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafan da suke fafatawa wasanni inda mafi yawan ‘yan wasan suka fara rataye takalmansu a ƙasashensu na haihuwa.
Sai dai Tevez ya bayyana cewar idan har ace zai ajiye takalmansa kuma sannan abashi dama ya gayyato ‘yan wasa domin su taka leda wajen murnar rataye takalman nasa to ya bayyana ‘yan wasan da zai gayyato a ɓangaren gidansa wanda zasu kara da kowacce ƙungiya ce.
Ga jerin ‘yan wasan da Tevez zai gayyato kamar haka:
Carlos Tevez ya ce zai gayyato Buffon da Hugo Ibarra da Rio Ferdinand da Gabriel Heinze da Patrice Evra da Paul Scholes da Andrea Pirlo da Paul Pogba da Cristiano Ronaldo da Leonel Messi da kuma Wayney Rooney.