By Abbas Yakubu Yaura
Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Yobe, Sanata Mohammed Hassan, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Hassan wanda aka fi sani da Dambu ya wakilci yankin Yobe ta kudu a majalisar dattawa. Ya koma APC ne a Abuja a hukumance inda Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Musamman na Jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya tarbe shi.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Sanata Ibrahim Bomoi na jam’iyyar (APC, Yobe ta Kudu), Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu da shugaban jam’iyyar APC na jiha, Alhaji Muhammadu Gadaka.
Mamman Mohammed, Darakta Janar na Hulda da Yada Labarai ga Buni a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ficewar tsohon dan majalisar ya haifar da mai ido ga jam’iyyar adawa a matakin jihohi da kasa baki daya.
“Sanata Dambu ya yi alkawarin biyayya da goyon bayansa ga shugabancin jam’iyyar a jihar da kuma yin aiki domin samun nasarar ta a dukkan matakai.
Sanarwar ta kara da cewa: “Motsawar Sanata Dambu zuwa cikin jam’iyyar zai kara wa jam’iyyar arzikin a shiyyar ‘B’ Sanata da kuma jihar.