Tsohon mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Westbrom-which Albion Alan Miller ya riga mu gidan gaskiya.
Kazalika Miller ya fafata wasa wa kungiyoyin Arsenal da Middlesbrough da kuma Ƙungiyar Blackburn Rovers cikin shekara 15 na zamanin kwallonsa wato daga 1988 zuwa 2003.
Har ila yau dan wasan ya kasnace cikin tawagarr Arsenal da ta lashe gasar FA da kuma kofin kalubale a shekarar 1993 gami sa kofin zakarun turai na European Cup Winners a shekarar 1994.
Dukkannin kungiyoyin da Miller ya buga musu wasa sun bayyana alhinin su bisa mutuwar tasa.