A ranar Talata ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida a wani katafaren gidansa dake Minna a jihar Neja.
Taron, wanda ya dauki kusan awa daya, watakila ba zai rasa nasaba da muradin Atiku a zaben 2023 ba.
Har yanzu dai Atiku bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba.
Bayan ganawa da Babangida, Atiku ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello.
Ya jajanta wa Gwamna Bello da al’ummar jihar kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
Atiku, a wata hira da manema labarai bayan ziyarar ban girma, ya ce ya je gidan gwamnati ne domin ziyarar ban girma.
Ya kara da cewa burinsa na 2023 zai fito fili idan lokaci ya yi.