Rohotanni dake shigowa Jaridar Dimokuraɗiyya na nuni da cewa Tsohon Ministan Noma da Albarkatun Ruwa na Najeriya Alhaji Abba Sayyadi Ruma, ɗan asalin Jahar Katsina ya rigamu gidan gaskiya.
Kamar yadda majiyar jaridar ta samu labari Marigayi Abba Sayyadi Ruma ya rasu ne a wata asibiti dake Birnin Landan, bayan ya ziyarci asibitin domin duba lafiyarshi.

KARANTA WANNAN LABARIN: Hisbah ta kama matashin da zai saida kanshi akan Naira miliyan 20
Marigayi Abba Sayyadi Ruma ya taba rike mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, kafin daga bisani ya zama Ministan Harkokin Noma Da Albarkatun Ruwa na Najeriya a lokacin Gwamnatin Marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua.
An haifi tsohon ministan a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 1962 a Karamar Hukumar Batsari.
Kafin rasuwarsa ya assasa Makarantar Koyon Kiwon Lafiya ta Cherish dake Batsari da Katsina.
Allah ya jikanshi da rahama.
Comments 1