Tsohon Ministan yada labarai a lokacin mulkin Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida Kuma tsohon Shugaban rundunar soji na jihar Rivers Brigediya Janar Anthony Ukpo Mai ritaya ya rasu.
Rahotanni sun nuna cewa, Birgediya Janar Anthony Ukpo ya rasu ne a safiyar yau Litinin.
Lauyan kuma Masani a fannin tsarin mulki kasa Leonard Anyogu, ne ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban sojojin ga manema labarai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kyauta Dillaliya ta bayyana irin mijin da takeso ta aura
Kazalika a makwanni biyu da suka gabata sai da yayyin shi biyu, suka rugamu gidan gaskiya.
Daga cikin su akwai, Madam Lydia wacce ta mutu a kasar Amurika, da kuma Shahararran Malamin addinin Kirista Joseph Edra Ukpo.
Anyogu ya bayyana cewa, Ukpo ya rasu ne a safiyar yau Litinin a wani asibiti, bayan ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya.
A wani labarin Kuma na daban a nan gida Nigeria
Wasu Alkalai za su amsa tambayoyi a gaban Alkalin alkalai a yau
Alkalin Alkalan Kasar nan Justice Tanko Muhammad a yau Litinin, zai tuhumi Manyan masu shari’a guda shida na jihohi daban-daban, bisa yanke hukunce hukuncen dake cin karo da juna..
Masu shari’an da za su gurfanar gaban Alkalin Alkalan sun hada da na jihar Rivers, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da kuma na jihar Imo.
Manyan jami’an Majalisar Shari’a ta kasa a jiya Lahadin, sun tabbatar da cewa,Alkalin Alkalan ya nemi bayanan shari’ar a cikin dukkan kararrakin da aka shigar, Wanda da daga baya aka fara samun sabani.
Justice Tanko ya kuma gayyaci babban alkalin jihar Delta, kan hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis din da ta gabata, na cire shugaban kwamitin riko na jam’iyar APC Mai Mulki, kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.
Kazalika akwai yuwuwar Alkalin Alkalan ya zauna taro, tare da Shuwagabannin kungiyar Lauyoyi na Kasa a wannan makon.