By Ishaq Dabai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, tace ta kama haramtattun magunguna sama da na naira miliyan 100 daga watan janeru zuwa watan Agusta.
Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi shine ya bayyana hakan ga manema labarai a yau litinin a Abuja, yace hukumar ta kama mutane 8,634 masu lafin yin safarar miyagun kwayoyi a tsakanin wadancan watanni da suka hadar da maza guda 6,461 da kuma mata guda 547.
Ya kara da cewa hukumar ta NDLEA ta lalata sama da gonakin tabar wiwi guda 1,202 daga sassa daban daban na kasar nan, baya da haka sama da kimanin ‘yan Najeriya mutane miliyan 10 ne suke ta’ammali da tabar wiwi da miyagun kwayoyi, a cewar bin ciken.
Babafemi yace “sama da mutane 8,634 da aka kama an samesu da kimanin kilogiram 2,776,000 na kwaya da kudinta ya kai naira miliyan 100 inda muka tabbatar da dakile wannan mummunan yanayin.
“Sannan mun kai kimanin mutane 1,630 wadanda aka yan kewa hukunci zuwa gidan kaso a cikin mutane 3,232 da ake tuhumarsu da laifuka daban daban, inda sama da masu ta ammali da kwayoyin su 4,269 aka basu shawara tare da dai dai ta musu hali daga janeru zuwa Agusta.