Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Vincent Ogbulafor ya mutu.
Ya rasu ne sakamakon matsalolin da suka shafi koda a wani asibiti a kasar Canada.
Mataimakin shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Abia Godfrey Onwuka ne ya bayyana haka bayan ya tattauna da matar marigayin Ifeoma Ogbulafor.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Ogbulafor kafin mutuwarsa ya taba cewa jam’iyyar PDP za ta kasance akan kargar mulkin kasar nan na tsahon shekaru 40 tun a wacen lokacin.
Onwuka ya bayyana mutuwar tasa a matsayin abu mai raɗaɗi, ya ƙara da cewa mutuwar Ogbulafor rashi ne ga al’umma baki ɗaya.
Ana sa ran dangin marigayin za su sanar da shirye-shiryen binne shi nan gaba kadan.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, A halin da ake ciki, gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom a wata sanarwa a ranar Asabar ya bayyana marigayin a matsayin dan jam’iyya na gaskiya.
A wani labarin kuma: Makarantu Sun Shiga Hutun Mako Shida Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa
A ci gaba da kokarin rage radadin ambaliyar ruwa a jihar Bayelsa, gwamnatin jihar ta ba da umarnin cewa, nan take daukacin makarantun firamare da sakandare na jihar su ci gaba da hutun makwanni shida.
Ana sa ran hutun ambaliya wanda ya zama wajibi ga makarantu masu zaman kansu da na gwamnati zai kare daliban daga duk wani mummunar illar da ambaliyar ta haifar.