Jam’iyyar PDP ta bayyana shirinta na kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2023 a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, 2022.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, a Abuja, ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Shugaban PDP Da Yace Jam’iyyar Za Tayi Mulkin Shekaru 40 Ya Mutu
Ya ce, “Jam’iyyar mu ta shirya tsaf don gudanar da yakin neman zabe da za a gudanar wanda dan takarar mu na Shugaban kasa, H E. Atiku Abubakar da abokin takararsa, H.E. Ifeanyi Okowa sun cika “Magana” don yaƙin neman zaɓe.
“Jam’iyyar PDP za ta kai kamfen din mu zuwa daukacin Jihohi, Kananan Hukumomi, Unguwa a fadin kasar nan a karkashin tsarin yakin neman zabe na bai daya kamar yadda kwamitin zartarwa na jam’iyyarmu (NEC) ya amince da shi.”
“Kamfen din mu zai kasance ne bisa jama’a da kuma mayar da hankali kan PDP da Burin Atiku Abubakar na Ceto, Ginawa da Mayar da Al’ummarmu daga Mummunan Mulkin Jam’iyyar APC.”
“Daga tuntubar da muka yi a shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida, a bayyane yake cewa ‘yan Nijeriya a fadin kasar nan, ba tare da la’akari da addini, kabila da ma siyasa ba, sun yarda da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, H.E. Atiku Abubakar a matsayin dan takara mafi kyawu mai gogewa a aikace, iya aiki, tsantsar tunani da son hadin kan al’ummarmu, inganta tattalin arzikin kasa, da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kasarmu.”
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa ‘yan Najeriya sun yi sha’awar fitowa rumfunan zabe domin kadawa Atiku Abubakar kuri’a a matsayin shugaban kasa saboda irin nasarorin da ya samu.
Ologunagba ya ci gaba da cewa, “H.E. Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban kasa Olusegun Obasanjo shine shugaban majalisar tattalin arzikin kasa.
“A lokacin; al’ummarmu ta sami nasarar samar da ayyukan yi na kasa wanda ba a taba ganin irinsa ba, An samu dala biliyan 30 na yafe bashin gaba daya daga kungiyoyin Paris da London Clubs.”
A wani labarin kuma, Makarantu Sun Shiga Hutun Mako Shida Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa
A ci gaba da kokarin rage radadin ambaliyar ruwa a jihar Bayelsa, gwamnatin jihar ta ba da umarnin cewa, nan take daukacin makarantun firamare da sakandare na jihar su ci gaba da hutun makwanni shida.
Ana sa ran hutun ambaliya wanda ya zama wajibi ga makarantu masu zaman kansu da na gwamnati zai kare daliban daga duk wani mummunar illar da ambaliyar ta haifar.