Sabon kocin Chelsea Thomas Tuchel ya kafa tarihin zama mai horas da kungiyar na farko cikin shekaru 16 da ya jagoranci wasanni 3 na farko bayan kama aiki ba tare da ya yi rashin nasara ba.
Tuchel ya kafa tarihin ne bayan doke kungiyar Tottenham da 1-0, yayin fafatwar da suka yi a gasar Firimiyar Ingila a ranar Alhamis.
Rabon da wani sabon koci ya samu irin wannan nasara a Chelsea tun cikin watan Agustan shekarar 2004, lokacin da Jose Mourinho ya karbi ragamar jagorancin kungiyar.
Yanzu haka Chelsea ce ta 6 a gasar Firimiya da maki 36.