A yammacin jiya ana gaf da za’a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasa a nahiyar turai akwai ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka sayi ‘yan wasa a sassa daban-daban na duniya musamman a manyan league da ake dasu guda biyar a nahiyar turai wato gasar Bundes Liga da gasar Laliga da gasar Serea A da gasar French League One da kuma gasar Premier ta ƙasar Ingila.
Sai dai jaridar www.dimokuradiyya.com.ng zata yi duba ne game da ‘yan wasan da aka saya a gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila a yammaci zuwa daren jiya da aka rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasan da aka yi siyayya sosai a ƙasar ta Ingila.
Sai dai za a iya cewa wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan suna cikin tsaka mai wuya duba da har yanzu basu sayi ‘yan wasan da zasu basu gudun nawar da suke da buƙata ba ganin cewar akwai sauran matsaloli a tattare da ƙungiyar ƙwallon ƙafan kama daga matsalar mai horas wa da kuma matsalar ‘yan wasa sosai da sosai.
Ga jerin yadda siyayyar ta kasance a daren na jiya a gasar ta ajin Firimiyar Ingila:
1. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal dake birnin London na ƙasar Ingila ta sayi ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid kuma ɗan asalin ƙasar Ghana wato Thomas Partey.
2. Ita kuwa Manchester United biyo bayan kashi da tasha a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham daci 6 da 1 a wasan mako na 4 na gasar ajin Firimiya yasa ta hasala ta sayo ‘yan wasa guda 4 rigis. ‘Yan wasan sune Edinson Cavani da Alex Telles da Amadu Diallo da kuma Facundo Pellistri.
3. Itama dai Southampton ta ɗakko
Theo Walcott daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton a matsayin aro.
4. Haka zalika itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta eeds United wadda ta sake dawowa gasar ajin Firimiya tun bayan shekaru 16 data koma gasa mai daraja ta biyu yasa ta sake dawowa gasar a kakar wasa ta bana, inda itama a yammacin na jiya ta sayo Raphina daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Rennes na ƙasar Faransa.
5. Itama dai Newcastle ta sayo Rodrigo Vilca a yammacin na jiya a yunƙurin gyara da takeyi.
6.Sannan itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton a ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Calor Ancelotti ta sayi Ben Godfrey daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Norwich City sannan kuma ta ɗakko ɗanwasa Robin Olsen a matsayin aro.
7. Ita kanta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fulham ba a bassu a bayaba domin suma sunyi kukan kura sun sayo Joachim Anderson a yayin hada-hadar rufe kasuwar sayen ‘yan wasan a yammacin na jiya.