Uba Sani Ya Tallafawa Mutane sama Dubu 30,000 da Kayayyakin Abinci a Jahar Kaduna
Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna Kuma Sanata Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Malam Uba Sani ya fara rabon kayan abinci kaso na farko, inda ya fara da buhunan shinkafa tirela 15 ga al’umma daban-daban a faɗin Ƙananan Hukumomi 23 na jihar Kaduna.
Sanata ya fara bada kayan Tallafin ne domin Albarkar wannan wata na azumin Ramadan, tare da tallafawa Al’umma su gudanar da Azumin su, cikin sauƙi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Ganduje ya umarci duk masu rike da mukaman siyasa su yi murabus
Wannan na Ƙunshe ne a cikin wata Sanarwa da Daraktan Dabarun Sadarwar Sanata Uba Sani, Ibrahim Salisu Abubakar ya fitar, yana mai cewa ana sa ran mutane dubu talatin 30,000 za su amfana da wannan rabon kayan Abinci na Sanata Uba sani.
Ana rabon kayan abincin ne ta hanyar
1. Shuwagabannin jam’iyyar kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.
2. Kungiyoyin Addini
3. Kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyi masu goyon bayan Sanata.
4. Da masu anfani da shafukan sada zumuntar zamani Social Media dana bugawa da sauransu.
5. Gidajen Marayu
6. Masu na ƙasa
7. Ma’aikata a dukkan ofisoshinsu da suka hada da babban ofishi da sauran nau’ikan mabukata na jihar ta kaduna.
“Wannan shi ne irin girma da martabar Sanata Malam Uba Sani wanda ya kasance ya kan aiwatar da koma a aikace ba a baki ba musamman a cikin watanni masu alfarma da lokutan bukukuwa al’adar addini” Inji Ibrahim
Sanatan ya kasance yana bada irin waɗannan kayayyakin Tallafin Abinci a kowace Shekara, domin sauƙaƙawa Al’ummar sa.
Sanata Uba Sani ya kasance Ɗan takarar Gwamna Mafi ƙarfi da kwarjini cikin ƴan takarar Gwamnan da suka bayyana ra’ayinsu na tsayawa takara a Jihar Kaduna.
Comments 1