Ukraine: Bayan Shafe Wata 19 Ana Yaƙi, Shugaba Zelensky ya kori ministan tsaro
Shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya kori Oleksii Reznikov, ministan tsaron kasar Ukraine.
A cewar shugaban kasar, kasar na bukatar “sababbin hanyoyi” yayin da yakin da Rasha ke shiga wata 19.
KARANTA WANNAN LABARIN:NLC Ta Nanata Ƙudirin Ta Na Shiga Yajin Aikin Gargaɗi
Zelensky ya bayyana hakan a ranar Litinin, yana mai cewa, “Na yanke shawarar maye gurbin ministan tsaron kasar Ukraine.
“Oleksii Reznikov ya yi kwanaki 550 ana gumurzun yaƙi da shi.”
Shugaban kasar ya zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Ukraine, Rustem Umerov, a matsayin wanda zai maye gurbin Reznikov.
Ministan tsaron da aka kora, Reznikov ya mika murabus dinsa a ranar Litinin.
A wani labarin kuma:Da Ɗumi-Ɗuminsa: Bayan Shafe Shekaru 40, Jirgin Ƙasan Lagos Ya Dawo Aiki
Gwamnatin jihar Legas ta fara gudanar da kasuwanci ta hanyar zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin shekaru bayan an fara aiwatar da shi a shekarar 1983.
A wani shirin kai tsaye da gidan talabijin na Channels TV da DAILY POST ta duba a ranar Litinin, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya fara hawa domin ƙaddamar da jirgin daga Marina zuwa Mile-2.