Da Ɗumi-Ɗuminsa: Bayan Shafe Shekaru 40, Jirgin Ƙasan Lagos Ya Dawo Aiki
Gwamnatin jihar Legas ta fara gudanar da kasuwanci ta hanyar zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin shekaru bayan an fara aiwatar da shi a shekarar 1983.
A wani shirin kai tsaye da gidan talabijin na Channels TV da DAILY POST ta duba a ranar Litinin, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya fara hawa domin ƙaddamar da jirgin daga Marina zuwa Mile-2.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ƙungiyar Likitocin Najeriya Ta Gargaɗi Gwamnatocin Kan Gagarumar Ambaliyar Ruwa Da Ke Tafe
Ku tuna cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da zangon farko na tashar jirgin kasa a Legas a watan Janairu.
Kashi na farko ya tashi daga Marina zuwa Mile 2 kuma yana da nisan kilomita 13.
Layin dogo mai tsawon kilomita 27 zai yi jigilar fasinjoji kusan 500,000 a kullum.
Kashi na farko yana da tashoshi biyar – Marina, National Theatre, Iganmu, Alaba da Orile.
Cikakken tafiya daga Marina zuwa Mile 2 zai ci N750, yayin da kudin shiyya – na fasinjojin da ba sa cikakken balaguron tafiya – zai kasance tsakanin N400 zuwa N500.
An samar da aikin gina layin dogo na Blue Line a shekarar 1983 lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Legas, Marigayi Alhaji Lateef Jakande.
An kaddamar da layin dogo bayan shekaru 20, lokacin gwamnatin Bola Tinubu a shekarar 2003
A wani labarin kuma:NLC Ta Nanata Ƙudirin Ta Na Shiga Yajin Aikin Gargaɗi
Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta ce tana ci gaba da shirye-shirye na shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga gobe, inda ta ce ba ta da masaniya kan wani taro da gwamnatin tarayya a yau.
Wani babban jami’in kungiyar ta NLC, ya shaida wa jaridar Vanguard a jiya cewa, ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata gayyata da Gwamnati ta yi domin gudanar da wani taro, inda ya kara da cewa majalisun jihohi da kungiyoyin ne suka dauki nauyin daukar wannan mataki na yajin aiki.