Gwamnan Jahar Borno Babagana Umara Zulum ya Ziyarci Ministan Noma da albarkantun Kasa Muhammad Sani Nanono domin tattaunawa akan kudirin gwamnatin tarayya na samar da wuraren kiwo ga Fulani. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Gwamna Zulum yacewa Ministan shi ya samar da filayen da za’a gina Ruga a karkashin hukumar bunkasa noma da kiwo.
Zulum ya bayyana hakane tare da goyon bayan kudirin gwamnatin tarayya na samar da filayen kiwo a gaba daya kasar.
KARANTA:- Matsalar Tsaro: Sarkin Musulmi da Malamai sun yi Addu’o’i na Musamman a Abuja
A tsammanin nanda dan lokaci kadan mahukunta daga hukumar bunkasa noma da albarkantun Kasa za su dira a Maiduguri don bada damar cigaba da aikin.
Minista Muhammad Sani Nanono ya yabawa gwamna Zulum kan irin jajircewarsa, ya kuma tabbatar masa za su kammala aikin.
Ya kuma nuna jindadinsa saboda ziyararsa da yayi.
A Ziyarar gwamna Zulum da yakai yana tare da kwamishina Modu Walama, da mai bashi shawara Tijjani Goni Modu da kuma kodinato na ruga Musa Inuwa Kubo