An zabi dan wasan Nigeria Victor Osimhen a matsayin gwarzon dan wasan Serie A na kasar Italiya a watan Satumba.
Osimhen ya farfado da nasara a farkon kakar shekarar 2021/2022 a watan Agusta, bayan da aka kore shi a wasan farko da Kungiyar shi ta Napoli ta fafata da Venezia, wanda hakan ya sa bai buga wasan da kungiyar ta buga da Genoa ba.
Tun daga wannan lokacin, dan wasan na Super Eagles ya zama abin tsoro ga masu adawa da shi, inda ya ci wa Napoli kwallaye bakwai a wasanni takwas da ya fafata mata, duk a watan Satumba.
Daga cikin kwallaye takwas da Dan wasan ya ci, a kakar wasa ta bana ya fafata da Udinese, tare da ci biyu da biyu, a karawarsu da Sampdoria sannan ya kara zura kwallo a raga a gasar Serie A, Napoli ta yi da Cagliari.
KARANTA WANNAN LABARIN: El-Rufa’i na daf da Rufe wasu Asibitoci da Makarantun Kiwon Lafiya a Kaduna
Kazalika Osimhen ya na ba da gudummawa tunda ga fara wasan Napoli na dari bisa dari, ta hanyar Nemo bugun daga Kai sai Mai tsaran raga biyu, ga tawagarsa.
A matakin nahiya, Osimhen shima ya zira kwallaye uku a gasar cin kofin Europa, inda ya zira kwallaye biyu a ragar Leicester City dake kasar Burtaniya a wasan su na farko a gasar.
Comments 1