Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen ya taya Super Eagles ta Najeriya murna bayan nasarar da suka yi akan Masar.
A karon farko Najeriya ta lallasa kasar Masar da suka fafata a gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan da ta sha kashi a a hannun Masar a shekarar 1963 da 2010.
Osimhen, wanda bai da tabbacin halartar sa gasar saboda raunin da ya samu a wasan da suka yi da Juventus, daga karshe an cire shi daga cikin tawagar bayan da Napoli ta bayyana cewa ya kamu da cutar ta COVID-19.
Tsohon dan wasan na Lille ya buga sakon taya murna ga takwarorinsa na Twitter, inda ya bukace su da su ci gaba da samun nasara a gasar.
“Barka da warhaka, mutane masu ban mamaki. Muna ci gaba da haɓaka kan wannan Nasarar,” ya rubuta.
Osimhen ya taka muhimmiyar rawa wajen samun tikitin shiga gasar AFCON ta 2021 a karkashin tsohon Kocin Najeriya Gernot Rohr.