Mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a jihar Bayelsa sun koka da halin da suke ciki yayin da suke komawa gidajensu bayan da gwamnatin jihar ta rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar a hukumance.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Gwamnatin jihar Bayelsa ta bude sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin jihar a yayin da ake fama da ambaliyar ruwa a watan jiya. Gwamnati ta kuma samar da abinci da sauran muhimman kayayyaki a sansanonin ga wadanda abin ya shafa.
Amma yayin da ruwan ya fara ja da baya, gwamnatin jihar a hukumance ta rufe sansanonin tare da mayar da mutanen gida, tare da ba wa kowannen su wata alama da za ta taimaka musu na komawa gida ranar Asabar.
KU KARANTA KUMA Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Garuruwa Sama Da 100 A Bayelsa
Sakamakon yadda yanayin tattalin arzikin da ya faru bayan ambaliyar ruwa ta rutsa da su, wasu ‘yan gudun hijirar sun shaida wa Daily trust a sansanin ‘yan gudun hijira na tafkin Oxbow cewa zai yi musu wuya su koma rayuwarsu ta yau da kullun, saboda duk wata hanyar rayuwarsu ta lalace.
Sun kuma yabawa gwamnatin jihar bisa wannan karamcin da ta yi musu na samar musu da matsuguni da ciyar da su a lokacin da ake fama da iftila’in.
Misis Esther Oyi ta roki Gwamna Douye Diri da ya taimaka musu su suka koma gida da tallafa musu da wasu kayan abinci da wani tallafin don ci gaba da sana’o’insu.
Ta ce: “Bari gwamna ya taimaka mana yayin da za mu je gida domin mu fara sabuwar rayuwa. Muna bukatar taimakonsa. Sun ciyar da mu sau biyu a rana, mun yaba. Bai kamata gwamnati ta bar mu mu koma gida hannu babu komai ba.”
Sauran wadanda ambaliyar ta shafa a sansanin da suka hada da Favour Christopher da Helen Olowu, sun godewa gwamnati bisa kulawar da ta ba su a sansanin, sannan sun bukaci gwamnatin jihar da ta taimaka wajen gyara abubuwan da suka lalace a yankunansu, domin su dawo su ci gaba da rayuwa kamar yadda ya kamata.
A Wani Labarin Kuma Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Ya Bada Tallafin Miliyan 50 A Jihar Jigawa
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.
Majiyar Dimokuradiyya ta bayyana cewa, Atiku ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr Nuhu Muhammad Sunusi a fadar sa a daren ranar Juma’a.