Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.
Majiyar Dimokuradiyya ta bayyana cewa, Atiku ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr Nuhu Muhammad Sunusi a fadar sa a daren ranar Juma’a.
Atiku ya ce dalilin da ya sa ya kai ziyarar shi ne domin jajanta wa jihar da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa bisa barnar da lamarin ya janyo a jihar.
KU KARANTA KUMA Atiku Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 55 A Jihar Bayelsa
Atiku wanda ya ziyarci fadar Sarkin Hadejia da wannan manufa, ya yi alkawarin dawowa yakin neman zabensa zagaye na biyu a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Ya ce Dutse da jihar Jigawa gidansa ne, kuma a duk lokacin da ya ga dama zai zo.
Da yake mayar da martani, mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr Nuhu Muhammadu Sunusi ya yaba da ziyarar da kuma bayar da gudunmawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Ya kuma tabbatarwa da dan takarar shugaban kasa na PDP cewa za a raba kudaden kai tsaye ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa domin kudin na da muhimmanci a gare su.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Hakazalika, Sarkin Hadejia, Adamu Abubakar Maje, ya kuma yabawa Atiku Abubakar bisa namijin kokarin da yake yi na ziyartar jihohin da ambaliyar ruwa ta afku.
A Wani Labarin Kuma Gwamna Bello Ya Kaddamar Da Rabon Litattafan Karatu Kyauta Ga Dalibai
Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya kaddamar da rabon litattafai 11,000 kyauta ga daukacin daliban manyan makarantun Sakandare (SSS 2) a makarantun gwamnati dake fadin jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ya ruwaito cewa, litattafan sun hada Chemistry da Physics kyauta, wanda Alh Ahmed Ododo, Babban Odita na Kananan Hukumomin Kogi, wanda ta dauki nauyi kuma ya bada tallafin don tallafawa shirin tallafin karatu da jagoranci na Gwamnatin Jihar.