Wadansu da ake zargin Yan bindiga ne sun farmaki tawagar Ganduje
Jami’an tsaro dake tafe da tawagar mai girma gwamanan Kano Abdullahi Ganduje sunyi musayar wuta da wadansu Yan bindiga kan hanyarsu ta dawowa daga Zamfara a daidai kan hanyar Shema dake jihar Katsina. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa.
Sai dai Gwamanan baya cikin tawagar lokacin da lamarin ya auku, Yan bindigan sun kulle kan hanyar Zamfara, Katsina da Kuma Kano a ranar Talata daidai garin Shema.
KARANTA:-Sanata Kabiru Marafa ya yi jurwaye Mai kama da wanka
A lokacin dai gwamna Ganduje na Zamfara wajan taya takwaransa gwamnan Zamfara da ya koma jam’iyyar APC.
Lokacin da lamarin ya auku, Yan sanda uku suka samu rauni sannan an farfasa Motoci da sharsashi.
Daga cikin akwai motar da tayar ta ta tashi aiki sanadiyyar harbin.
Sai dai sunyi kokarin kaita gefe guda bayan abin ya lafa aka gyara.