Hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta yammacin Afrika, wato WAEC ta nada Pateh Bah daga kasar Gambiya, a matsayin sabon magatakardar hukumar har na tsawon shekara biyar. .
Wannan sanarwar na fitowa ne daga Abiodun Aduloju, Daraktan hulda da kafafen watsa labarai na Hedikwatar hukumar WAEC dom dale birnin Accra dake kasar Ghana, ya ce; nadin na sa zai fara aiki ne daga watan Oktoban 2019 zuwa watan Satumban 2024.
Bah dai ya gaji Dr Iyi Uwadiae, wanda wa’adinsa ya kare a ranar 30 ga watan Satumban shekararnan.