Wamakko, Dambuwa, Lamido sun sami Tikitin Tsayawa Takarar Sanatocin Sokoto
Tsohon Gwamnan Jahar Sokoto Sanata Aliyu Wamakko ya sake samun nasarar lashe zaben Fidda Gwani na Sanatan Sokoto ta Arewa .
Tsohon Gwamnan ya samu nasarar tare da Sanata mai Wakiltar Sokoto ta Kudu Danbaba Dambuwa, da Alhaji Ibrahim Lamido ba tare da abokanan hamayya ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Jirgi ɗauke da Mutane 22 yayi ɓatan Dabo a sararin samaniya a Nepal
Dayake magana a lokacin da yake ayyana sakamakon, Kwamitin Zaɓen ƙarƙashin jagorancin Sakataren Barista Wale Ojo da Mamban Kwamitin Dr. Tona Famadewa yace kasancewar Wamakko shi kaɗai ne Ɗan Takara ya samu nasarar samun Tikitin Tsayawa Takara na Jam’iyyar bayan yarda da Delegates 420 Suka Yi a fadin Ƙananan Hukumomi 8 da suka ƙunshi Shiyyar.
Sanatan wanda shine Jagoran Jam’iyyar APC a Jahar ya samu Tikitin Tsayawa Takara ne kashi na uku a Majalisar Dattijai a ƙarƙashin Jam’iyar.
Wannan nasarar Wamakko ya biyo bayan yarda da Deliget suka yi wanda wani Babangida Dantsoho yayi, tare da amince war Aliyu Sabo daga Ƙaramar Hukumar Ƙware.
Dayake jawabi bayan ya samu nasara, Sanata Wamakko ya bayyana Jindaɗinsa tare da yabawa Deliget da suka nuna goyon bayan su, domin cigaban shi da sauran ƴan Takarar.
Comments 1