Wani Jirgi ɗauke da Mutane 22 yayi ɓatan Dabo a sararin samaniya a Nepal
Wani Jirgi mai ɗaukar Fasinja 22 yayi ɓatan Dabo a Nepal ranar Lahadi, kamar yadda Jami’ai suka bayyana cewa, rashin Kyakkyawan yanayi ya haifar da ɓacewar Jirgin.
Jirgin mai ƙirar Twin Otter ya tashi ne daga yammacin garin Pokhara zuwa Jomson da misalin ƙarfe 9:55 na safe, amma Jirgin ya rasa hanya bayan mintuna 15 da tashi.
“Muna ƙoƙarin mu gano ina yankin da Jirgin yake”, inji Mai Magana da Yawun Kamfanin Jirgin Tara Air Sudarshan Bartaula, ya Shaidawa Kamfanin Dillancin Labaru na AFP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Samun nasarar Atiku, APC zata iya shan kaye a 2023 — Sanatan APC, Orji Kalu
“Jami’an gudanar da ceto da Ƴan Sanda nata yin bakin ƙoƙari domin gano wurin da Jirgin ya nufa”.
Yace Akwai Fasinjoji 19 a ciki da Ma’aikata 3. Fasinjojin sun ƙunshi ƴan Jamani guda biyu da ƴan Ƙasar Indiya guda 4, sauran kuma ƴan Ƙasar Nepali.
Jomson ya Kasance sanannen wuri ne a Himalayas, mintuna 20 a saman Jirgi daga Pokhara, Wanda yakai Kilomita 200 a yammacin garin Kathmandu.
Phanindra Mani Pokharel, Mai Magana da Yawun Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, yace an tura Jirage masu saukar ungulu domin dubo inda Jirgin yake.
Amma yace ba’a gani abubuwa sosai.
“Rashin Kyakkyawan yanayi zai iya lalata binciken da ake yi. Rashin ganin yayi yawa, zai iya kawo cikas ga aikin nemo Jirgin,” Inji Pokharel.
Comments 1