Wani Ƙazamin Faɗa Ya Sake Ɓarkewa Tsakanin ISWAP Da B/Haram A Jihar Borno
Wani kazamin fada ya sake barkewa tsakanin bangaren marigayi Abubakar Shekau na Boko Haram da kungiyar IS a yammacin Afirka a ranar Alhamis wanda ya kai ga kashe wani kwamanda da aka bayyana sunansa “Kundu” da kuma mayakan da dama.
Fadan dai ya faru ne a tsakanin kananan hukumomin Dikwa da Bama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Amusan Ta Karbi Kyautar OON A Yayin Da Buhari Ya Karrama ‘Yan Wasan Najeriya
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, Kundu da tawagarsa suna aikin fashi ne lokacin da ISWAP suka kama su a kan babura shida, kowannensu na dauke da mayaka uku.
Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro da masu tada kayar baya a tafkin Chadi ya tabbatar da wannan fadan.
Ya ce, “An gwabza kazamin fada tsakanin ‘yan ta’addan wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama a bangaren ‘yan ta’addan na Boko Haram, yayin da ‘yan ta’addar ISWAP kadan suka samu raunuka.
“‘Yan ta’addar Boko Haram sun kai ga barin baburansu ga ‘yan ta’addar ISWAP.”
A wani labarin kuma, sojojin Najeriya sun kai farmaki a yankunan ISWAP a wasu hare-hare da suka kai inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama ciki har da kwamandoji uku a yankin tafkin Chadi.
An samu labarin cewa jiragen yakin sojin kasar Super Tucano da ke karkashin hadin gwiwa na rundunar sojojin sama na Operation Hadin Kai sun lalata sansanoni uku a yankin arewacin jihar Borno.
An tattaro cewa an kaddamar da hare-haren ne da rundunar sojojin sama ta Operation Hadin Kai ta shirya a maboyar ‘yan ta’addan a Rino, Jibularam da Kangarwa a kananan hukumomin Marte da Kukawa da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Satumba.
Wani babban jami’in soji ya shaida wa wakilinmu cewa an kashe mayaka da dama a wasu hare-hare ta sama da aka kai a tafkin Chadi tsakanin Talata zuwa Alhamis.
Makama, wanda shi ma ya tabbatar da ayyukan, ya bayyana cewa, harin da aka kai ta sama ya yi barna na farko ya nufi maboyar ‘yan ta’addan da kuma wani sansanin horo a Rinu, inda ya kashe mayakan da ba a tantance adadinsu ba.
Majiyoyi sun ce ATF ta sake kai wani harin bam a Jibularam wanda ya yi sanadin kashe kwamandojin ISWAP uku da wasu mayaka da dama.
Wata majiya ta bayyana sunayen kwamandojin da Muhammed Balge, babban mai gabatar da kara; Malam Chiroma, wanda shi ne shugabansa na biyu; da kuma Amir Bashir, aka Iblis, wanda ya kasance maharbi kuma dan ta’addar.
“A wani abin kuma, wanda ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar soji ta Operation Hadin Kai ta samu, sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama da ke tafiya cikin motoci biyu a cikin Kangarwa a karamar hukumar Kukawa.
“Lokacin da aka samu kiran tashin hankalin, nan da nan jirgin na NAF ya ruga zuwa wurin da suka kama tare da kashe ‘yan ta’adda da dama. Dakarun da aka girke a yankin ya nuna cewa ‘yan ta’addar sun yi mummunar barna sakamakon harin da jiragen suka kai,” in ji majiyar sojojin.
A wani labarin kuma: 2023: An Nada Wike A Kwamitin Kamfen Na Shugaban Kasa A PDP, Tambuwal Ne DG
Duk da zargin da ake yi cewa Arewa ta dauki nauyin rike madafun iko a jam’iyyar PDP, jam’iyyar ta nada Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a matsayin babban Darakta na Kwamorin yakin neman zabe na Shugaban Kasa (PCO) a zaben 2023.
Yayin da Tambuwal ke matsayin babban Darakta na Kwamitin yakin neman zabe na Kasa (NCMC), Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom shi ne Shugaban yakin neman zaben Shugaban Kasa (PCC).