Kwanturolan da ke kula da Sashin Samar da Kasuwanci na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Anthony Ayalogu, ya rasu.
Daily Post ta ruwaito cewa, An ce Ayalogu ya yi fama da rashin lafiya a filin jirgin saman Malam Aminu Kano ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Janye Yajin Aikin ASUU: Jami’ar Obafemi Awolowo Ta Sanya Ranar Cigaba Da Karatu
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban na Kwastam din ya yanke jiki ya fadi ne, inda aka garzaya da shi Asibitin Sojojin Sama da ke Kano, inda anan ne aka tabbatar da rasuwarsa da misalin karfe 8:20 na daren jiya.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, AA Maiwada na sashin hulda da jama’a na ta Kwastam, ya ce, “Ya na kan hanyar wucewa ne a wani aiki na hukumar kwatsam, kuma ya yi rashin lafiya da ya isa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, sai ya yanke jiki ya fadi. Duk kokarin da aka yi na ceto rayuwarsa abun ya ci tura domin ya mutu ne a ranar Litinin 17 ga Oktoba, 2022 a Asibitin Sojan Sama na Najeriya 465 a Kano. Ya kasance yana da shekaru 57.”
Mamacin Dan asalin karamar hukumar Onitsha ta Arewa da ke jihar Anambra ne, Ayalogu ya yi karatun digiri na farko a fannin Botany daga jami’ar Fatakwal.
Ya shiga aikin hukuma ga Kwastam ne a ranar 24 ga Satumba, 1991 a matsayin Mataimakin Sufurtanda.
Shugaban Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya jajantawa ‘yan uwa da abokan arzikin marigayi Ayalogu, inda ya ce za a yi kewarsa matuka.
“Muna addu’ar Allah ya baiwa iyalan Ayalogu kwarin guiwar jure wannan rashi mara misaltuwa.”
A WANI LABARIN KUMA: Yan bindiga Sun Kashe Mai Unguwa, Da Wasu Mutum 2 Tare Da Garkuwa Da Wasu Da Dama
Wasu mutane ɗauke da bindigogi da ake kyau tata zaton yan bindiga ne sun kashe shugaban garin Nyaluna dake ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.
Daily Post ta ruwiaito cewa, Maharan sun kuma farmaki wasu garuruwa biyu dake yankin.