Wani Babban Kamfanin Mai na Turawa, ya shirya ficewa daga Najeriya
Kamfanin Shell na Birtaniya, ya amince ya sayar da reshen shi wato SPDC na Najeriya, ya sanar da shirin ficewa daga Najeriyar.
Wani babban kamfanin mai na kasa da kasa wato Shell ya amince ya sayar da reshensa na Shell Petroleum Development Company of Nigeria Limited SPDC ga wasu haɗakar kamfanoni biyar da ke Najeriya da kuma wani kamfanin makamashi ta kasa da kasa kan kudi har dala biliyan 24.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Wannan matakin na nufin kawo ƙarshen aikin babban kamfanin na Mai na kasar Burtaniya a Najeriya tun bayan kafuwar shi a shekarar 1979.
Sai dai kamfanin ya bayyana cewa kammala cinikin yana jiran amincewar Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke da kashi 55 cikin 100 na hannun jari da kuma wasu sharudda.
KARANTA NAN:Daukar Aiki: PSC ta tantance ƴan sanda dubu 136,177
Da yake bayani dangane da matakin, Shell ya lura cewa za a sake wasu sabbin tsare-tsare a Kamfanin biyo bayan canjin ikon mallakar.
Waɗannan sun haɗa da tsarin gudanar da aiki cikin kwarewa, amfani da sabuwar fasaha a matakai waɗanda Kamfanin ke aiwatarwa a madadin duka kamfanonin da ke da hakkin mallaka a yanzu.
A halin da ake ciki, sanarwar ta fayyace cewa ma’aikatan Kamfanin za su ci gaba da daukar ma’aikata a kamfanin yayin da yake komawa zuwa sabon mallaka.
Kamfanin ya ce yana ci gaba da taka rawar gani wajen tallafawa gudanar da ayyukan Kamfanin da kuma kamfanonin da suka yi haɗaka wajen mallakar shi domin samar da wani kaso mai tsoka na iskar gas ga Najeriya wato LNG da NLNG don taimakawa Najeriya ta samu mafi girman darajar daga Iskar Gas.
Daraktan Kamfanin Shell Zoë Yujnovich Shell’s yayin da yake magana game da aikin kamfanin na gaba, ya ce zai mai da hankali kan saka hannun jari a kan zurfin ruwa da ayyukan iskar gas.
Wannan yarjejeniya ta kasance wani muhimmin ci gaba ga kamfanin na Shell a Najeriya wanda ya yi daidai da aniyarmu da aka sanar a baya na ficewa daga hako mai a yankin Neja-Delta don sauƙaƙa ayyukan mu tare da mai da hankali kan ingantaccen saka hannun jari a Najeriya kan matsayinmu na amfani da ruwa domin samar da Gas.
Shell na ganin kyakkyawar makoma a Najeriya tare da kyakkyawan hangen nesa na saka hannun jari ga bangaren makamashin ta, za mu ci gaba da tallafawa ci gaban bukatun makamashin kasar Najeriya da kuma burin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a yankunan da suka dace da dabarunmu.”